12
Kuɓuta mai banmamakin da Bitrus ya yi daga kurkuku
Kusan a wannan lokaci ne Sarki Hiridus ya kama waɗansu da suke na ikkilisiya, da niyya ya tsananta musu. Ya sa aka kashe Yaƙub, ɗan’uwan Yohanna, da takobi. Sa’ad da ya ga wannan ya faranta wa Yahudawa rai, sai ya kama Bitrus shi ma. Wannan ya faru kwanakin Bikin Burodi Marar Yisti. Bayan ya kama shi, sai ya sa shi a kurkuku, ya danƙa shi a hannun soja hurhuɗu kashi huɗu, don su yi gadinsa. Hiridus ya yi niyyar ya yi masa shari’a a gaban mutane bayan Bikin Ƙetarewa.
Saboda haka aka tsare Bitrus a kurkuku, amma ikkilisiya ta nace da addu’a ga Allah dominsa.
A daren da in gari ya waye da Hiridus yake niyyar kawo shi domin a yi masa shari’a, Bitrus yana barci tsakanin sojoji biyu, daure da sarƙoƙi biyu, masu gadi kuma suna bakin ƙofa. Ba zato ba tsammani sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana haske kuma ya haskaka a ɗakin. Ya bugi Bitrus a gefe ya kuma tashe shi ya ce, “Maza, ka tashi!” Sarƙoƙin kuwa suka zube daga hannuwansa.
Sa’an nan mala’ikan ya ce masa, “Ka sa rigunarka da takalmanka.” Bitrus kuwa ya sa. Mala’ikan ya faɗa masa cewa, “Ka yafa mayafinka ka bi ni.” Bitrus ya bi shi suka fita kurkukun, amma bai ma san cewa abin da mala’ikan yake yi tabbatacce ne ba; yana tsammani wahayi yake gani. 10 Suka wuce masu gadi na fari da na biyu, suka kuma isa ƙofar ƙarfe ta shiga birni. Ƙofar kuwa ta buɗe musu da kanta, suka kuma wuce. Sa’ad da suka yi tafiya tsawon wani titi, nan take mala’ikan ya bar shi.
11 Sai Bitrus ya dawo hankalinsa ya ce, “Yanzu na sani ba shakka Ubangiji ne ya aiki mala’ikansa yă cece ni daga hannun Hiridus da kuma dukan mugun fatan Yahudawa.”
12 Da ya gane haka, sai ya tafi gidan Maryamu uwar Yohanna, wanda ake kuma kira Markus, inda mutane da yawa suka taru suna addu’a. 13 Bitrus ya ƙwanƙwasa ƙofar waje, sai wata mai aiki a gidan da ake kira Roda ta zo tă ji ko wane ne. 14 Da ta gane muryar Bitrus, ta cika da murna ta gudu ta koma ba tare da ta buɗe ƙofar ba, sai ta koma a guje ta ce da ƙarfi, “Ga Bitrus a bakin ƙofa!”
15 Sai suka ce mata, “Kina hauka.” Da ta nace cewa shi ne, sai suka ce, “To, lalle, mala’ikansa ne.”
16 Amma Bitrus ya yi ta ƙwanƙwasawa. Da suka buɗe ƙofar suka kuma gan shi, sai suka yi mamaki. 17 Bitrus ya yi musu alama da hannunsa su yi shiru sai ya bayyana yadda Ubangiji ya fitar da shi daga kurkuku. Ya ce, “Ku gaya wa Yaƙub da kuma ’yan’uwa game da wannan,” sa’an nan ya tashi ya tafi wani wuri.
18 Da safe, hargitsin da ya tashi tsakanin sojojin ba ƙarami ba ne, a kan abin da ya sami Bitrus. 19 Bayan Hiridus ya neme shi bai same shi ba, sai ya tuhumi masu gadin, ya kuma ba da umarni a kashe su.
Mutuwar Hiridus
Sa’an nan Hiridus ya tashi daga Yahudiya ya tafi Kaisariya ya kuma yi ’yan kwanaki a can. 20 Yana da rashin jituwa da mutanen Taya da na Sidon; sai suka haɗa kai suka nemi ganawa da shi. Bayan suka sami goyon bayan Bilastus, amintaccen bawan sarki, sai suka nemi salama, domin sun dogara ga ƙasar sarkin don samun abincinsu.
21 A ranar da aka shirya Hiridus, sanye da kayan sarautarsa, ya zauna a gadon sarautarsa ya kuma ya wa mutanen jawabi. 22 Suka tā da murya suka ce, “Wannan muryar wani allah ne, ba ta mutum ba.” 23 Nan take, domin Hiridus bai yi wa Allah yabo ba, wani mala’ikan Ubangiji ya buge shi, tsutsotsi kuwa suka cinye shi ya kuma mutu.
24 Amma maganar Allah ta ci gaba da ƙaruwa ta kuma bazu.
An aiki Barnabas da Shawulu
25 Sa’ad da Barnabas da Shawulu suka kammala aikinsu, sai suka komo daga* Urushalima, tare da Yohanna, wanda ake kira Markus.
* 12:25 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā zuwa