6
Zaɓen mutane bakwai
1 A waɗannan kwanaki, sa’ad da yawan almajirai suke ƙaruwa, sai Yahudawan masu jin Hellenanci a cikinsu suka yi gunaguni a kan Yahudawan da suke Ibraniyawa domin ba a kula da gwaurayensu a wajen raba abinci na yau da kullum.
2 Saboda haka Sha Biyun nan suka tara dukan almajirai wuri ɗaya, suka ce, “Bai zai yi kyau mu bar hidimar maganar Allah don mu shiga hidimar abinci ba.
3 ’Yan’uwa, ku zaɓi mutum bakwai daga cikinku waɗanda aka sani suna cike da Ruhu da kuma hikima. Mu kuwa za mu danƙa musu wannan aiki
4 mu kuwa mu mai da halinmu ga yin addu’a da kuma hidimar maganar Allah.”
5 Wannan shawarar kuwa ta gamshi dukan ƙungiyar. Sai suka zaɓi Istifanus, mutumin da yake cike da bangaskiya da kuma Ruhu Mai Tsarki; da Filibus, Burokorus, Nikano, Timon, Farmenas, da Nikolas daga Antiyok, wanda ya tuba zuwa Yahudanci.
6 Suka gabatar da waɗannan mutane wa manzanni, waɗanda kuwa suka yi addu’a, suka ɗibiya hannuwansu a kansu.
7 Saboda haka maganar Allah ta yaɗu. Yawan almajirai a Urushalima kuwa ya yi saurin ƙaruwa, firistoci masu yawa kuma suka zama masu biyayya ga wannan bangaskiya.
An kama Istifanus
8 To, Istifanus, mutum cike da alheri da ikon Allah, ya aikata manyan ayyukan da alamu masu banmamaki a cikin mutane.
9 Sai hamayya ta taso daga ’yan ƙungiyar Majami’a na ’Yantattu (kamar yadda ake kiransu), Yahudawan Sairin da Alekzandariya da kuma lardunan Silisiya da Asiya. Mutanen nan suka fara muhawwara da Istifanus,
10 amma ba su iya cin nasara kan hikimarsa ko kuma a kan Ruhu wanda ta wurinsa ne ya magana ba.
11 Sa’an nan a asirce suka zuga waɗansu mutane su ce, “Mun ji Istifanus ya faɗa kalmomin saɓo game da Musa da kuma Allah.”
12 Ta haka suka tā da hankalin mutane da dattawa da kuma malaman dokoki. Suka kama Istifanus suka kawo shi a gaban Majalisa.
13 Suka kawo masu ba da shaidar ƙarya, waɗanda suka ba da shaida cewa, “Wannan mutum ba ya rabuwa da maganar banza a kan wurin nan mai tsarki da kuma doka.
14 Gama mun ji shi yana cewa wannan Yesu Banazare zai rushe wurin nan ya kuma canja al’adun da Musa ya ba mu.”
15 Dukan waɗanda suke zaune a Majalisar suka kafa wa Istifanus ido, suka kuma ga fuskarsa ta yi kama da ta mala’ika.