Kolossiyawa
1
1 Bulus, wanda Allah ya zaɓa don yă zama manzon Kiristi Yesu, da kuma daga Timoti ɗan’uwanmu,
2 Zuwa ga tsarkaka da kuma amintattun ’yan’uwa cikin Kiristi da suke a Kolossi.
Alheri da salama daga Allah Ubanmu, su kasance tare da ku.
Godiya da addu’a
3 Kullum muna gode wa Allah, Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, sa’ad da muke addu’a dominku.
4 Gama mun ji labarin bangaskiyarku a cikin Yesu Kiristi da kuma ƙaunar da kuke yi saboda dukan tsarkaka.
5 Kuna yin haka ne kuwa domin abin da kuke bege yana a ajiye a sama. Kun riga kun ji game da wannan bege sa’ad da kuka gaskata saƙon nan na gaskiya wanda shi ne bisharar
6 da ta zo muku. Ko’ina a duniya wannan bishara tana yi ta haihuwa tana kuma girma, kamar yadda take yi a cikinku tun daga ranar da kuka ji ta kuka kuma fahimci alherin Allah cikin dukan gaskiyarta.
7 Kun koyi wannan gaskiya daga wurin Efafaras, ƙaunataccen abokin hidimarmu, wanda yake amintacce mai hidimar Kiristi a madadinmu,
8 wanda kuma ya faɗa mana ƙaunar da kuke yi cikin Ruhu.
9 Shi ya sa tun daga ranar da muka sami labarin, ba mu fasa yin addu’a dominku ba. Kullum muna roƙon Allah yă sa ku san kome da yake so ku yi, domin ku sami hikima ta Ruhu, ku kuma sami ganewar kome duka.
10 Ta haka za ku yi rayuwa wadda ta dace da Ubangiji, ku kuma gamshe shi a ta kowace hanya, kuna yin aiki mai kyau ta kowace hanya, kuna kuma yin girma cikin sanin Allah.
11 Allah yă ƙarfafa ku da dukan iko bisa ga ɗaukakar ƙarfinsa domin ku kasance da jimrewa sosai da kuma haƙuri, cikin farin ciki
12 kuna gode wa Uba, wanda ya sa kuka cancanci ku sami rabo a gādon tsarkaka a cikin mulkin haske.
13 Gama ya riga ya cece mu daga mulkin duhu ya kuma kawo mu cikin mulkin Ɗan da yake ƙauna,
14 wanda ta wurinsa muka sami fansa da kuma gafarar zunubai.
Fifikon Kiristi
15 Kiristi shi ne surar da ake gani na Allah wanda ba a iya gani, ɗan fari a kan dukan halitta.
16 Ta wurinsa aka halicci dukan abu, abubuwan da suke cikin sama da abubuwan da suke a duniya, waɗanda ake gani, da waɗanda ba a gani, ko kursiyoyi ko ikoki ko masu mulki ko hukumomi; an halicci dukan abu ta wurinsa da kuma dominsa ne.
17 Ya kasance kafin dukan abu, kuma a cikinsa ne dukan abubuwa suke a harhaɗe.
18 Shi ne kuma kan ikkilisiya, wadda take jikinsa. Shi ne mafari da kuma na farko da ya tashi daga matattu, domin a cikin kowane abu yă zama mafifici.
19 Gama Allah ya ji daɗi yă sa dukan cikarsa ta kasance a cikin Kiristi,
20 ta wurin Kiristi ne ya komar da kome zuwa ga kansa. Ya kawo salama ga abubuwan da suke ƙasa da abubuwan da suke sama, ta wurin jinin Kiristi da ya zubar a kan gicciye.
21 A dā kuna a ware da Allah, kuka kuma zama abokan gāba a cikin tunaninku saboda mugun halinku.
22 Amma Ɗansa ya zama mutum ya kuma mutu. Saboda haka Allah ya yi sulhu da ku, yanzu kuwa ya bar ku ku tsaya a gabansa da tsarki, marasa aibi, da kuma marasa abin zargi.
23 Sai ku ci gaba cikin bangaskiyarku, kuna tsaye a kafe kuma tsayayyu, ba tare da gusawa daga begen da kuka ji daga bishara ba. Wannan ita ce bisharar da kuka ji wadda aka yi shelarta ga kowace halittar da take ƙarƙashin sama, wadda kuma ni Bulus, na zama mai hidimarta.
Hidimar Bulus ga ikkilisiya
24 Yanzu, ina farin ciki saboda wuyar da nake sha dominku, don ta wurin wuyan nan zan cika abin da ya rage na wuyar da Kiristi ya sha saboda jikinsa, wato, ikkilisiya.
25 Na zama mai hidimar ikkilisiya bisa ga aikin nan da Allah ya ba ni amana saboda ku, domin in sanar da maganar Allah sosai.
26 Wannan magana da nake gaya muku asiri ne da yake a ɓoye tun zamanai masu yawa, wanda yanzu aka bayyana ga tsarkaka.
27 Su ne Allah ya so yă sanar da yadda irin yalwar ɗaukakar asirin nan take a cikin al’ummai, asirin nan kuwa shi ne Kiristi a cikinku, begen ɗaukakar da za a bayyana.
28 Saboda haka ko’ina muka tafi, muna shela, muna gargaɗi, muna kuma koyar da kowa da dukan hikima, don mu miƙa kowa cikakke a cikin Kiristi.
29 Don haka ne ina fama, ina kuma ƙoƙari da duk ƙarfin nan da Kiristi ya ba ni.