10
Wahayin Daniyel na mutum
A shekara ta uku ta Sairus sarkin Farisa, sai aka ba wa Daniyel (wanda ake kira Belteshazar) wahayi. Saƙon kuwa gaskiya ce wadda take tattare da babban yaƙi. Fahimtar saƙon ya zo masa a cikin wahayi.
A wannan lokaci ni Daniyel na yi makoki har na sati uku. Ban ci abinci mai kyau ba; ba nama ko ruwa inabin da ya shiga bakina; kuma ba na amfani da man shafawa gaba ɗaya har sai da sati nan uku suka wuce.
A rana ta ashirin da huɗu ga watan farko, a sa’ad da nake tsaye a bakin babban kogi, Tigris, na ɗaga kaina na duba sai ga wani mutum tsaye sanye da rigar lilin, ya yi ɗamara da zinariya zalla daga Ufaz kewaye da ƙugunsa. Jikinsa kamar lu’ulu’u yake, fuskarsa kuma kamar walƙiya, idanunsa kamar harshen wuta, hannuwansa da ƙafafunsa kamar gogaggiyar tagulla, muryarsa kuma kamar amon babban taron jama’a.
Ni, Daniyel, kaɗai ne na ga wahayin; mutanen da suke tare da ni ba su gani ba, amma wata irin babbar razana ta auko musu har suka gudu suka ɓuya. Sai aka bar ni ni kaɗai, ina juyayi wannan babban wahayi, ba ni da sauran ƙarfi, fuskata ta yamutse kuma ba ni da sauran ƙarfi. Sai na ji yana magana, da ina sauraronsa, sai na shiga barci mai nauyi, na kuwa fāɗi rubda ciki.
10 Sai hannu ya taɓa ni ya sa makyarkyata a hannuna da ƙafafuna. 11 Sai ya ce, “Daniyel, kai ne wanda ake ƙauna sosai, ka yi lura da kyau game da kalmomin da zan yi maka magana a kansu, ka tashi yanzu, gama an aiko ni a gare ka.” Sa’ad da ya faɗa mini haka, sai na tashi a tsaye ina rawan jiki.
12 Sai ya ci gaba da cewa, “Kada ka ji tsoro, Daniyel. Gama tun daga ran da ka fara sa zuciya ga neman ganewa, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Allahnka, an ji addu’arka, amsar addu’arka ce ta kawo ni. 13 Amma mai mulkin masarautar Farisa ya tsare ni har kwana ashirin da ɗaya. Sai da Mika’ilu, ɗaya daga cikin manya shugabanni, ya zo ya taimake ni, saboda an tsare ni a can tare da sarkin Farisa. 14 Yanzu na zo domin in bayyana maka abin da zai faru da mutanenka nan gaba, gama wahayin ya shafi lokacin da bai riga ya zo ba ne.”
15 Yayinda yake faɗin mini haka, sai na sunkuyar da kaina ƙasa shiru, ba magana. 16 Sai wani wanda ya yi kama da mutum* ya taɓa leɓunana, na kuma buɗe bakina sai na fara magana. Na ce wa wannan da yake tsaye a gabana, “Na cika da azaba saboda wannan wahayi, ranka yă daɗe, ina kuma neman taimako. 17 Yaya ni bawanka zan iya magana da kai, ranka yă daɗe? Ƙarfina ya ƙare kuma ina numfashi da ƙyar.”
18 Har yanzu wannan wanda yana kama da mutum ya taɓa ni ya kuma ba ni ƙarfi. 19 Ya kuma ce, “Kada ka ji tsoro, ya kai mutumin da ake fahariya, salama a gare ka! Ka ƙarfafa yanzu; ka yi ƙarfin hali.”
Sa’ad da ya yi magana da ni, sai na samu ƙarfi na ce, “Ka yi magana ranka yă daɗe, tun da yake ka sa na sami ƙarfi.”
20 Sai ya ce mini, “Ka san abin da ya kawo ni gare ka? Ba da jimawa ba zan koma in yi yaƙi da mai mulkin Farisa, kuma idan na tafi, mai mulkin Hellenawa zai taso; 21 amma da farko zan faɗa maka abin da aka rubuta a cikin Littafin Gaskiya (Babu wanda ya taimake ni yaƙi da waɗannan sai dai Mika’ilu, sarkinku.
* 10:16 Yawancin rubuce-rubucen hannu na Nassin Masoretik; ɗaya daga cikin rubuce-rubucen Masoretik, Naɗaɗɗen littafin Mataccen Teku da kuma Seftuwajin Sa’an nan wani abu kamar hannun mutum