8
1 Wa yake kama da mai hikima?
Wa ya san bayanin abubuwa?
Hikima takan haskaka fuskar mutum,
ta kuma kawo sakin fuska.
Ka yi wa sarki biyayya
2 Ka yi biyayya da umarnin sarki, na ce, saboda alkawarin da ka yi a gaban Allah.
3 Kada ka yi hanzarin tashi daga gaban sarki. Kada ka kāre abin da ba daidai ba, gama zai iya yin duk abin da ya ga dama.
4 Da yake maganar sarki ita ce mafificiya, wa zai iya ce masa, “Me kake yi?”
5 Duk wanda ya yi biyayya da umarninsa ba zai sami lahani ba,
zuciya mai hikima kuma zai san lokacin da ya dace da kuma hanyoyin da suka fi.
6 Gama akwai lokaci da hanyoyin da suka dace da yin kowane abu,
ko da yake wahalar mutum ta yi masa yawa.
7 Da yake ba wanda ya san nan gaba,
wa zai iya faɗa masa abin da zai faru?
8 Ba wanda yake da iko a kan iska har da zai riƙe ta,
saboda haka babu mai iko kan ranar mutuwarsa.
Kamar yadda ba a sallamar mutum a lokacin yaƙi,
haka ma mugunta ba za tă saki masu aikata ta ba.
9 Na ga dukan waɗannan, yayinda na lura da kowane abin da ake yi a duniya. Akwai lokacin da mutum yakan nauyaya wa waɗansu ba da sonsa ba.
10 Sa’an nan kuma, na ga an binne masu mugunta, waɗanda suke shiga da fita daga tsattsarkan wuri suke kuma samun yabo a birnin da suka yi wannan. Wannan ma ba shi da amfani.
11 In ba a hanzarta aka yanke hukunci a kan laifi ba, zukatan mutane sukan cika da ƙulle-ƙullen aikata abubuwan da ba daidai ba.
12 Ko da yake mugu ya aikata laifi ɗari ya kuma yi tsawon rai, na san cewa zai fi wa masu tsoron Allah kyau, waɗanda suke girmama Allah.
13 Duk da haka, domin masu mugunta ba su ji tsoron Allah ba, abubuwa ba za su yi musu kyau ba, ransu kamar inuwa yake ba zai yi tsawo ba.
14 Akwai kuma wani abu marar amfani da yake faruwa a duniya, masu adalci sukan sha hukuncin da ya dace da masu mugunta, masu mugunta kuma sukan karɓi sakayyar da ya cancanci masu adalci su samu. Na ce, wannan ma, ba shi da amfani.
15 Saboda haka abin da na ce, shi ne mutum yă ji daɗi, domin iyakar jin daɗinsa a wannan rai, shi ne yă ci, yă sha, yă ji wa kansa daɗi. Aƙalla yana iya yin wannan in ya yi aiki a kwanakin da Allah ya ba shi a wannan duniya.
16 Da na mai da hankalina don in sami hikima in kuma lura da wahalar mutum a duniya, ko da a ce idanunsa ba sa barci dare da rana,
17 sam, ba zai taɓa fahimci abin da Allah yake yi ba. Iyakar ƙoƙarin da ka yi duk ba za ka iya ganewa ba. Masu hikima suna iya cewa sun sani, amma kuwa ba su sani ba.