22
Zunubin Urushalima
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
 
“Ɗan mutum, za ka shari’anta ta? Za ka shari’anta wannan birni mai kisankai? To, sai ka kalubalance ta da dukan ayyukanta na banƙyama ka kuma ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce ya birnin da take kawo wa kansa hallaka ta wurin kisankai a cikinta kina kuma ƙazantar da kanki ta wurin yin gumaka, kin zama mai laifi saboda jinin da kika zubar kika kuma zama ƙazantacciya ta wurin gumakan da kika yi. Kin kawo kwanakinki ga ƙarshe, kuma ƙarshen shekarunki sun zo. Saboda haka zan mai da ke abar ba’a ga al’ummai da abin dariya ga dukan ƙasashe. Waɗanda suke kusa da waɗanda suke nesa za su yi miki ba’a, ya ke birni marar kunya, cike da rigima.
“ ‘Duba yadda kowane yerima Isra’ila waɗanda suke cikinki yake yin amfani da ikonsa yana kisankai. A cikinki sun rena mahaifi da mahaifiya; a cikinki sun zalunci baƙo suka wulaƙanta maraya da gwauruwa. Kin rena abubuwana masu tsarki kika kuma ƙazantar da Asabbataina. A cikinki akwai mutane waɗanda suka nace su yi kisankai; a cikinki akwai waɗanda suke ci a dutsen tsafi suna yin ayyukan lalata. 10 A cikinki akwai waɗanda suke kwana da matan mahaifansu; a cikinki akwai waɗanda suke kwana da mata a lokacin da suke al’adarsu, sa’ad da suke da rashin tsarki. 11 A cikinki mutum guda yakan yi laifi abin ƙyama da matar maƙwabcinsa, wani cikin rashin kunya ya ƙazantar da matar ɗansa, wani kuma ya kwana da ’yar’uwansa, ’yar mahaifinsa. 12 A cikinki mutane suna karɓan cin hanci don su yi kisankai; kina ba da rance da ruwa da ƙari, kina kuma cin riba a kan maƙwabcinki ta wurin ƙwace. Kina kuma manta da ni, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
13 “ ‘Tabbatacce zan tafa hannuwana a kan ƙazamar riba da kika ci da jinin da kin zubar a cikinki. 14 Ƙarfin halinki zai jure ko kuwa hannuwanki za su yi ƙarfi a ranar da na gamu da ke? Ni Ubangiji na faɗa, zan kuma aikata. 15 Zan watsar da ke cikin al’ummai in warwatsa ke cikin ƙasashe; zan kuma kawo ƙarshen rashin tsarkinki. 16 Sa’ad da ki ƙazantu* a idanun al’umma, za ki san cewa ni ne Ubangiji.’ ”
17 Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 18 “Ɗan mutum, gidan Isra’ila ta zama ƙwan maƙera a gare ni; dukansu tagulla ne, kuza, ƙarfe da darma da suka rage a tanderu. Su ƙwan maƙerar azurfa ne kawai. 19 Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin ku duka kun zama ƙwan maƙera, zan tattara ku a Urushalima. 20 Kamar yadda mutane sukan tattara azurfa, tagulla, ƙarfe, darma da kuza a cikin tanderu don su narkar da su da wuta, haka zan tattara ku cikin fushina da kuma hasalata in sa ku cikin birnin in narkar da ku. 21 Zan tattara ku zan kuma hura muku wutar hasalata, za ku kuma narke a cikinta. 22 Kamar yadda azurfa kan narke a tanderu, haka za ku narke a cikinta, kuma za ku san cewa Ni Ubangiji na zubo muku da zafin fushina.’ ”
23 Har yanzu maganar Ubangiji ta zo gare ni cewa, 24 “Ɗan mutum, ka faɗa wa ƙasar, ‘Ke ƙasa ce marar ruwan sama ko yayyafi a ranar hasala.’ 25 Akwai haɗin bakin sarakunanki a cikinki kamar rurin zaki mai yayyage ganimarsa; suna cin mutane, suna kwashe dukiya da abubuwa masu daraja suna mai da yawanci gwauraye a cikinki. 26 Firistocinki suna karya dokokina, sun ƙazantar da tsarkakan abubuwana; ba sa bambanta tsakanin tsarki da marar tsarki; suna koyarwa cewa babu bambanci tsakanin marar tsarki da mai tsarki; suna kuma rufe idanunsu ga kiyaye Asabbataina, da haka suke saɓon sunana. 27 Shugabanninki a cikinki suna kama da kyarketai masu yayyage ganimarsu; suna kisa suna kuma kashe mutane don samun ƙazamar riba. 28 Annabawanki sun yi wa waɗannan ayyuka shafe da farar ƙasa ta wurin wahayin ƙarya da duban ƙarya. Suna cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa’ alhali kuwa Ubangiji bai faɗa ba. 29 Mutanen ƙasar na yin ƙwace suna yin fashi; suna cin zalin matalauta da mabukata suna wulaƙanta baƙo suna hana musu adalci.
30 “Na nemi mutum guda a cikinsu wanda zai gina katanga ya tsaya a gabana a tsakani a madadin ƙasar don kada in hallaka ta, amma ban sami ko ɗaya ba. 31 Saboda haka zan zuba hasalata a kansu in cinye su da wutar fushina, ina ɗora alhakin ayyukansu a bisa kawunansu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”
* 22:16 Ko kuwa Sa’ad da na raba ki da gādonki