24
Tukunyar dahuwa
1 A shekara ta tara, a wata na goma, a rana ta goma, maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2 “Ɗan mutum, ka rubuta wannan rana, wannan rana, domin sarkin Babilon ya yi ƙawanya wa Urushalima a wannan rana.
3 Ka faɗa wa wannan gidan ’yan tawaye wani misali ka kuma faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“ ‘Ka sa tukunyar dahuwa; ka sa ta a kan wuta
ka kuma zuba ruwa a cikinta.
4 Ka sa gunduwoyin nama a cikinta
dukan gunduwoyi masu kyau, cinya da kafaɗa.
Ka cika ta da waɗannan ƙasusuwa mafi kyau;
5 ka kama mafi kyau daga cikin garken.
Ka tara itace a ƙarƙashinta saboda ƙasusuwan;
ka sa ta tafasa
ka kuma dafa ƙasusuwan a cikinta.
6 “ ‘Gama wannan shi ne abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“ ‘Kaito birnin nan mai zubar da jini,
ga tukunya wadda take da tsatsa,
wadda tsatsarta ba za tă fita ba!
Ka fitar da shi gunduwa-gunduwa
ba tare da jefa ƙuri’a a kansu ba.
7 “ ‘Gama zubar da jini yana a tsakiyarta,
ta zubar da shi a dutsen da yake a fili;
ba tă zubar da shi a ƙasa ba,
inda ƙura za tă rufe shi.
8 Don a zuga hasala a kuma yi sakayya
na sa jininta a dutsen da ba a rufe ba,
saboda kada a rufe.
9 “ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“ ‘Kaito birnin nan mai zubar da jini!
Ni ma zan jibge itace da yawa.
10 Ka tula gumagumai
ka kuma ƙuna wuta.
Ka dafa naman da kyau,
kana haɗawa da yaji;
ka kuma bar ƙasusuwan su ƙone.
11 Sa’an nan ka sa tukunyan nan da babu kome a kan garwashi
sai ta yi zafi har darmarta ta yi ja wur
domin dattinta ya narke
tsatsarta kuma ta ƙone.
12 Ta gajiyar da dukan ƙoƙari;
ba a fid da tsatsarta nan mai yawa ba,
kai, ko a wuta ma.
13 “ ‘Yanzu ƙazantarki ita ce lalaci. Domin na yi ƙoƙari in tsabtacce ke amma ba ki tsabtattu daga ƙazantarki ba, ba za ki ƙara yin tsabta ba sai hasalata a kanki ya kwanta.
14 “ ‘Ni Ubangiji na faɗa. Lokaci ya zo da zan aikata. Ba zan janye ba; ba zan ji tausayi ba, ba kuwa zan bari ba. Za a hukunta ki bisa ga hali da ayyukanki, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
Matar Ezekiyel ta rasu
15 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
16 “Ɗan mutum, da farat ɗaya ina gab da ɗauke abin da idanunka suke jin daɗin gani. Duk da haka kada ka yi makoki ko ka yi kuka ko ka zub da hawaye.
17 Ka yi nishi shiru; kada ka yi makoki saboda matacciyar. Ka naɗa rawaninka ka kuma sa takalmanka a ƙafa; kada ka rufe sashen fuskarka daga ƙasa ko ka ci abincin da masu kuka sukan ci.”
18 Da gari ya waye, sai na yi magana da mutane, da yamma kuwa matata ta rasu. Kashegari na yi yadda aka umarce ni.
19 Sai mutane suka tambaye ni suka ce, “Ba za ka faɗa mana abin da waɗannan abubuwa suke nufi a gare mu ba?”
20 Sai na ce musu, “Maganar Ubangiji ta zo mini cewa
21 faɗa wa gidan Isra’ila, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gab da ƙazantar da wuri mai tsarkina, kagarar da kuke taƙama, abin da idanunku suke jin daɗin gani, abin faranta zuciyarku. ’Ya’yanku maza da mata waɗanda kun bari a baya za su mutu ta wurin takobi.
22 Za ku kuma yi yadda na yi. Ba za ku rufe sashe ƙasa na fuskarku ko ku ci abinci da masu kuka sukan ci ba.
23 Za ku naɗa rawunanku a kai ku sa takalmanku a ƙafafunku. Ba za ku yi kuka ko makoki ba amma za ku lalace saboda zunubanku ku kuma yi ta yin nishi.
24 Ezekiyel zai zama alama gare ku; za ku yi daidai yadda ya yi. Sa’ad da wannan ya faru, za ku san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.’
25 “Kai kuma ɗan mutum, a ranar da zan ɗauke musu kagararsu, farin cikinsu da darajarsu, abin da idanunsu ke jin daɗin gani, abin da yake faranta musu zuciya, da kuka ’ya’yansu maza da mata,
26 a ranan nan wanda ya tsere zai zo don yă ba ka labari.
27 A lokacin bakinka zai buɗe, za ka yi magana da shi ba kuwa za ka ƙara yin shiru ba. Ta haka za ka zama alama gare su, za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji.”