28
Annabci a kan sarkin Taya
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka faɗa wa mai mulkin Taya cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“ ‘Cikin alfarmar zuciyarka
ka ce, “Ni allah ne;
ina zama a kan kursiyin allah
a tsakiyar tekuna.”
Amma kai mutum ne ba allah ba,
ko da yake ka ɗauka kana da hikima kamar allah.
Ka fi Daniyel hikima ne?*
Ba asirin da yake ɓoye a gare ka?
Ta wurin hikimarka da ganewarka
ka sami dukiya wa kanka
ka kuma tara zinariya da azurfa
cikin wuraren ajiyarka.
Ta wurin dabararka mai girma cikin kasuwanci
ka ƙara dukiyarka,
kuma saboda dukiyarka
zuciyarka ta cika da alfarma.
“ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“ ‘Domin ka ɗauka kai mai hikima ne,
mai hikima kamar allah,
zan kawo baƙi a kanka,
waɗanda suka fi mugunta cikin sauran al’ummai;
za su zāre takubansu a kan kyakkyawar hikimarka
su kuma ɓarke darajarka mai walƙiya.
Za su jefar da kai cikin rami,
za ka kuwa yi muguwar mutuwa
a tsakiyar tekuna.
Za ka iya ce yanzu, “Ni allah ne,”
a gaban waɗanda suka kashe ka?
Za ka zama mutum kurum, ba allah ba,
a hannuwan waɗanda suka kashe ka.
10 Za ka yi mutuwar marar kaciya
a hannuwan baƙi.
Na faɗa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
 
11 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 12 “Ɗan mutum, ka yi makoki domin sarkin Taya ka kuma ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“ ‘Ka kasance hatimin cikakke,
cike da hikima da cikakke a kyau.
13 Ka kasance a Eden,
a lambun Allah;
aka yi maka ado da kowane dutse mai daraja,
yakutu, tofaz, da zumurrudu,
kirisolit, onis da yasfa,
saffaya, turkuwoyis da beril.
Tsare-tsare da shirye-shiryenka an yi su da zinariya ne;
a ranar da aka halicce ka an shirya su.
14 An shafe ka kamar kerub mai tsaro,
gama haka na naɗa ka.
Kana a tsattsarkan dutsen Allah;
ka yi tafiya a tsakiyar duwatsun wuta.
15 Ka kasance marar laifi cikin dukan hanyoyinka
daga ranar da aka halicce ka
sai da aka sami mugunta a cikinka.
16 Ta wurin yawan kasuwancinka
ka cika da rikici,
ka kuma yi zunubi.
Saboda haka na kore ka da kunya daga dutsen Allah,
na kore ka, ya kerub mai tsaro,
daga cikin duwatsun wuta.
17 Zuciyarka ta cika da alfarma
saboda kyanka,
ka kuma lalace hikimarka
saboda darajarka.
Saboda haka na jefar da kai zuwa ƙasa;
na sa ka zama abin kallo a gaban sarakuna.
18 Ta wurin yawan zunubanka da kasuwancinka na cuta
ka ƙazantar da wuri mai tsarkinka.
Saboda haka na sa wuta ta fito daga cikinka,
ta cinye ka,
na maishe ka toka a bisa ƙasa
a kan idon dukan waɗanda suke kallonka.
19 Dukan al’umman da suka san ka
sun giggice saboda masifar da ta auko maka;
ka zo ga mummunar ƙarshe
ba za ka ƙara kasancewa ba har abada.’ ”
Annabci a kan Sidon
20 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 21 “Ɗan mutum, ka fuskanci Sidon; ka yi annabci a kanta 22 ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“ ‘Ina gāba da ke, ya Sidon,
zan sami ɗaukaka a cikinki.
Za su san cewa ni ne Ubangiji,
sa’ad da na zartar da hukunci a kanta
na kuma nuna kaina mai tsarki a cikinta.
23 Zan aika da annoba a kanta
in kuma sa jini ya zuba a titunanta.
Kisassu za su fāɗi a cikinta,
da takobi yana gāba da ita a kowane gefe.
Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.
24 “ ‘Mutanen Isra’ila ba za su ƙara kasance da mugayen maƙwabta waɗanda za su zama sarƙaƙƙiya masu zafi da ƙaya mai tsini ba. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.
25 “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa sa’ad da na tattara mutanen Isra’ila daga al’ummai inda suke a warwatse, zan nuna kaina mai tsarki a cikinsu a idon al’ummai. Sa’an nan za su zauna a ƙasarsu, wadda na ba wa bawana Yaƙub. 26 Za su zauna a can lafiya su kuma gina gidaje su nome gonakin inabi; za su zauna lafiya sa’ad da zan zartar da hukunci a kan dukan maƙwabtansu da suka wulaƙanta su. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji Allahnsu.’ ”
* 28:3 Ko kuwa Danel; yadda aka rubuta Ibraniyanci na wannan suna zai yi kamar ana zance wani dabam ne da annabi Daniyel. 28:13 Ko kuwa lafis lazuli