8
Bautar gumaka a cikin haikali
A shekara ta shida, a wata shida a ranar ta biya, yayinda nake zaune a gidana dattawan Yahuda kuma suna zaune a gabana, hannun Ubangiji Mai Iko Duka ya zo a kaina a can. Na duba, sai na ga siffa kamar na mutum.* Daga kwankwaso zuwa ƙasa ya yi kamar wuta, kuma daga kwankwaso zuwa sama kamanninsa ya yi haske yana ƙyalli kamar ƙarfe mai haske. Ya miƙa abin da ya yi kamar hannu ya kama a gashin kaina. Ruhu ya ɗaga ni tsakanin sama da ƙasa, a cikin wahayoyi kuma Allah ya ɗauke ni zuwa Urushalima, zuwa ƙofa zuwa gabas na cikin fili, inda gunki mai tsokanar kishi yake tsaye. A can gabana kuwa ga ɗaukakar Allah na Isra’ila, kamar a wahayin da na gani a fili.
Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, duba waje arewa.” Sai na duba, a mashigin arewa na ƙofar bagaden kuwa na ga wannan gunki na tsokanar kishi.
Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ga abin da suke yi, abubuwan banƙyamar da gidan Isra’ila ke yi a nan, abubuwan da za su kore ni daga wuri mai tsarkina? Amma za ka ga abubuwan da suka ma fi banƙyama.”
Sa’an nan ya kawo ni mashigin filin. Na duba, na kuma ga rami a bango. Ya ce mini, “Ɗan mutum, yanzu ka haƙa cikin bangon.” Da na haƙa cikin bangon sai na ga ƙofar shiga a can.
Sai ya ce mini, “Shiga ka ga mugaye da kuma abubuwa banƙyamar da suke yi a can.” 10 Na kuwa shiga na duba, sai na ga zāne-zāne ko’ina a bangon na kowane irin abubuwa masu rarrafe da kuma dabbobi masu ƙazanta da dukan gumakan gidan Isra’ila. 11 A gabansu ga dattawa saba’in na gidan Isra’ila tsaye a cikinsu, Ya’azaniya ɗan Shafan kuwa yana tsaye a cikinsu. Kowa yana da farantin ƙona turare a hannunsa, tulin hayaƙin turare mai ƙanshi ya tunnuƙe zuwa sama.
12 Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ga abin da dattawan gidan Isra’ila suke yi a cikin duhu, kowa yana a ɗakin tsafin gunkinsa? Suna cewa, ‘Ubangiji ba ya ganinmu; Ubangiji ya yashe ƙasar.’ ” 13 Ya kuma ce, “Za ka gan su suna yin abubuwan da suka fi waɗannan banƙyama.”
14 Sa’an nan ya kawo ni mashigin arewa na ƙofar gidan Ubangiji, sai na ga mata zaune a can, suna makokin Tammuz. 15 Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ga wannan? Za ka ga abubuwan da suke masu banƙyama fiye da wannan.”
16 Sa’an nan ya kawo ni cikin fili na cikin gidan Ubangiji, a can kuwa a ƙofar haikali, tsakanin shirayi da bagade, akwai kamar mutum ashirin da biyar. Suka ba haikalin Ubangiji baya suna fuskanta wajen gabas, suna rusuna wa rana a gabas.
17 Ya ce mini, “Ka ga wannan, ɗan mutum? Ƙaramin abu ne gidan Yahuda su yi abubuwan banƙyamar da suke yi a nan? Dole ne su cika ƙasar da rikici su kuma ci gaba da tsokane ni in yi fushi? Dube su suna tsokanata! 18 Saboda haka zan hukunta su cikin fushi; Ba zan dube su da tausayi ko kuwa in ƙyale su ba. Ko da yake suna ihu a kunnuwana, ba zan saurare su ba.”
* 8:2 Ko kuwa na ga siffa mai kamanni wuta