25
Hadayu don tabanakul
(Fitowa 35.4-9)
Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa su kawo mini hadaya. Za ka karɓi hadaya daga hannun kowane mutum wanda zuciyarsa ta yarda yă bayar.
 
“Ga iri jerin kayan da za ka karɓo daga hannunsu,
 
“zinariya, da azurfa, tagulla,
shuɗi, shunayya da jan zare, lallausan lilin,
da gashin akuya,
fatun ragunan da aka wanke, fatun awaki masu kyau,
itacen akashiya,
mai domin fitila,
kayan yaji domin man keɓewa da kuma turare mai ƙanshi,
da duwatsun Onis, da duwatsun da za a mammanne a efod da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
 
“Sa’an nan ka sa su yi mini wuri mai tsarki, domin in zauna a cikinsu. Ka ƙera wannan tabanakul da duk kayan da suke ciki da waje, daidai yadda zan nuna maka.
Akwatin alkawari
(Fitowa 37.1-9)
10 “Ka sa a yi akwatin alkawarin da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kuma kamu ɗaya da rabi. 11 Ka dalaye shi da zinariya zalla ciki da waje, za ka yi wa gefe-gefensa ado da gurun zinariya. 12 Ka kewaye akwatin da zoban zinariya huɗu ka kuma haɗa su da ƙafafunsa huɗu, zobai biyu a kowane gefe. 13 Sa’an nan ka yi sanduna da itacen ƙirya, ka dalaye su da zinariya. 14 Ka sa sandunan a cikin zoban, a gefen akwatin domin ɗaukansa. 15 Sanduna za su kasance a cikin waɗannan zoban akwatin alkawarin; ba za a cire su ba. 16 Sa’an nan ka sa Shaidar da zan ba ka, a cikin akwatin.
17 “Ka yi murfin kafara da zinariya zalla, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kuma kamu ɗaya da rabi. 18 Ka kuma yi kerubobi biyu da zinariyar da aka ƙera, ka sa a gefen nan biyu na murfin. 19 Ka yi kerubobi biyu, ɗaya a wannan gefe, ɗaya kuma a ɗayan gefen; za ka manne su a kan murfin, su zama abu ɗaya. 20 Kerubobin su kasance da fikafikansu a buɗe, domin su inuwantar da murfin, za su fuskanci juna, suna duba murfin. 21 Ka sa murfin a bisa akwatin ka kuma sa allunan dokokin alkawarin da zan ba ka a ciki. 22 Can, a bisa murfin da yake tsakanin kerubobi biyu da suke bisa akwatin alkawari na Shaida, zan sadu da kai, in kuma ba ka dukan umarnai domin Isra’ilawa.
Tebur
(Fitowa 37.10-16)
23 “Ka yi tebur da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu, fāɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa kuma kamu ɗaya da rabi. 24 Ka dalaye shi da zinariya zalla ka kuma yi masa ado kewaye da gurun zinariya. 25 Ka yi dajiya mai fāɗin tafin hannu, ka kuma yi wa dajiyar ado da gurun zinariya. 26 Ka yi zoban zinariya huɗu domin teburin, ka daure su a kusurwoyi huɗu, inda ƙafafu huɗun suke. 27 Zoban za su kasance kusa da dajiyar don riƙe sandunan da za a yi amfani don ɗaukar teburin. 28 Ka yi sandunan da itacen ƙirya, ka dalaye su da zinariya, da sandunan ne za ku riƙa ɗaukan teburin. 29 Da zinariya zalla kuma za ka yi farantansa, da kwanoninsa na tuya, da butocinsa, da kwanoninsa domin zuban hadayu. 30 Ka sa burodin Kasancewa a kan wannan tebur, yă kasance a gabana kullum.
Wurin ajiye fitila
(Fitowa 37.17-24)
31 “Ka yi wurin ajiye fitilar da zinariya zalla, ka kuma yi gindinsa tare da gorar jikinsa da ƙerarriyar zinariya; kwafunansa da suka yi kamar furanni, tohonsa da furanninsa su yi yadda za su zama ɗaya da shi. 32 Wurin ajiye fitilar yă kasance da rassa shida, rassan nan za su miƙe daga kowane gefe na wurin ajiye fitilan, uku a gefe guda, uku kuma a ɗaya gefen. 33 Kwafuna uku masu siffar furanni almon, da toho, da kuma furannin za su kasance a rashe guda, uku a kan rashe na biye, haka kuma a kan saura rassan shida da suka miƙe daga wurin ajiye fitilan. 34 A bisa wurin ajiye fitilan kuwa za a kasance da kwafuna huɗu masu siffar furannin almon, da toho, da furanni. 35 Toho ɗaya zai kasance a ƙarƙashin rassa biyu na farkon da suka miƙe daga wurin ajiye fitilan, toho na biyu a ƙarƙashin rassa biyu na biye, toho na uku a ƙarƙashin rassa na uku, rassa shida ke nan duka. 36 Tohon da kuma rassan za su kasance ɗaya da wurin ajiye fitilan da aka yi da ƙerarriyar zinariya.
37 “Sa’an nan ka yi fitilu bakwai, ka sa su a bisa wurin ajiye fitilan ta yadda za su haskaka wajen da suka fuskanta. 38 Za a yi lagwaninsa da manyan farantansa da ƙerarriyar zinariya. 39 Da zinariya zalla na talenti ɗaya za ka yi wurin ajiye fitilan da waɗannan abubuwa duka. 40 Sai ka lura ka yi su daidai bisa ga fasalin da aka nuna maka a kan dutse.