47
Yusuf ya tafi yă faɗa wa Fir’auna, “Mahaifina da ’yan’uwana, tare da garkunansu da shanunsu da kome da suke da shi, sun zo daga ƙasar Kan’ana, suna kuwa a Goshen yanzu.”
Sai ya zaɓi mutum biyar daga cikin ’yan’uwansa, ya gabatar da su a gaban Fir’auna.
Fir’auna ya tambayi ’yan’uwan, “Mece ce sana’arku?”
Suka amsa wa Fir’auna suka ce, “Bayinka makiyaya ne, kamar yadda kakanninmu suke.” Suka kuma ce masa, “Mun zo, mu zauna a nan na ɗan lokaci, gama yunwa ta yi tsanani a Kan’ana, dabbobin bayinka kuma ba su da wurin kiwo. Saboda haka yanzu, muna roƙonka, bari bayinka su zauna a Goshen.”
Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Mahaifinka da ’yan’uwanka sun zo maka, ƙasar Masar kuma tana gabanka, ka zaunar da mahaifinka da ’yan’uwanka a sashe mafi kyau na ƙasar, bari su zauna a Goshen. Idan kuma ka ga waɗansu a cikinsu da suka fi dacewa, sai ka sa su lura mini da shanuna.”
Sa’an nan Yusuf ya shigar da Yaƙub mahaifinsa, ya gabatar da shi a gaban Fir’auna. Bayan Yaƙub ya albarkaci* Fir’auna, sai Fir’auna ya tambaye shi, “Shekarunka nawa da haihuwa?”
Yaƙub kuwa ya ce wa Fir’auna, “Shekarun hijirata, shekaru ɗari da talatin ne. Shekaruna kaɗan ne cike da wahala, ba za a kuwa daidaita su da shekarun hijirar kakannina ba.” 10 Sai Yaƙub ya albarkaci Fir’auna, ya yi masa bankwana, sa’an nan ya fita.
11 Ta haka Yusuf ya zaunar da mahaifinsa da ’yan’uwansa a Masar, ya ba su mallaka a sashe mafi kyau na ƙasar, a yankin nan na Rameses, kamar yadda Fir’auna ya umarta. 12 Yusuf ya kuma tanada wa mahaifinsa da kuma ’yan’uwansa da dukan gidan mahaifinsa, abinci bisa ga yawan ’ya’yansu.
Hidimar Yusuf a lokacin yunwa
13 A yanzu, a cikin ƙasar duka, ba abinci, gama yunwa ta yi tsanani ƙwarai, har ƙasar Masar da ƙasar Kan’ana suka shiga matsananciyar wahala! 14 Yusuf ya tattara dukan kuɗaɗen da suke a Masar da Kan’ana don biyan hatsin da suke saya, ya kuwa kawo su a fadan Fir’auna. 15 Sa’ad da kuɗin mutanen Masar da Kan’ana suka ƙare, dukan Masar ta zo wurin Yusuf ta ce, “Ka ba mu abinci. Me zai sa mu mutu a idanunka? Kuɗinmu duk sun ƙare.”
16 Yusuf ya ce, “To, ku kawo dabbobinku, zan sayar muku da abinci a madadin dabbobinku, tun da kuɗinku ya ƙare.” 17 Saboda haka suka kawo dabbobinsu wa Yusuf, ya kuma ba su abinci a madadin dawakai, tumaki da awaki, shanu da jakunansu. Ya kuwa ba su abinci a madadin dabbobinsu, a wannan shekara.
18 Sa’ad da wannan shekara ta ƙare, sai suka zo wurinsa a shekara ta biye suka ce, “Ba za mu ɓoye maka ba ranka yă daɗe, kuɗinmu sun ƙare, dabbobinmu kuma sun zama naka. Ranka yă daɗe, in ban da jikunanmu da gonakinmu, ba abin da ya rage mana. 19 Kada ka bar mu mu mutu, ka yi wata dabara! Kada ka bari mu rasa gonakinmu. Ka musaye mu da abinci, mu da gonakinmu. Mu kuwa za mu zama bayin Fir’auna. Ka ba mu iri don mu rayu, kada mu mutu, don kuma kada gonakin ƙasarmu su zama kango.”
20 Ta haka Yusuf ya saya wa Fir’auna ƙasar Masar duka, gama Masarawa duka sun sayar da gonakinsu, saboda yunwa ta tsananta musu. Ƙasar ta zama mallakar Fir’auna. 21 Yusuf kuwa ya mai da mutanen bayi, daga wannan iyakar Masar zuwa wancan. 22 Amma bai sayi gonakin firistoci ba, gama suna karɓa rabo daga Fir’auna ne, suna kuma da isashen abinci daga rabon da Fir’auna yake ba su. Dalilin ke nan da ba su sayar da gonakinsu ba.
23 Yusuf ya ce wa mutane, “Yanzu da na saye ku da kuma gonakinku a yau wa Fir’auna, ga iri don ku shuka a gonaki. 24 Amma sa’ad da hatsi suka nuna, za ku ba da kashi ɗaya bisa biyar ga Fir’auna. Sauran kashi huɗu bisa biyar kuma ku riƙe a matsayin iri don gonaki da kuma abinci wa kanku da gidajenku da kuma ’ya’yanku.”
25 Suka ce, “Ka ceci rayukanmu, in ya gamshe ka, ranka yă daɗe, za mu zama bayin Fir’auna.”
26 Ta haka Yusuf ya kafa wannan ya zama doka game da ƙasa a Masar, har yă zuwa yau cewa kashi ɗaya bisa biyar na amfani gona ya zama na Fir’auna. Gonakin firistoci ne kaɗai ba su zama na Fir’auna ba.
27 To, Isra’ilawa suka zauna a Masar a yankin Goshen. Suka mallaki filaye a can, suka riɓaɓɓanya suka ƙaru ƙwarai.
28 Yaƙub ya yi zama a Masar shekaru goma sha bakwai, yawan shekarunsa duka sun zama ɗari da arba’in da bakwai. 29 Sa’ad da lokaci ya gabato da Isra’ila zai mutu, sai ya kira ɗansa Yusuf, ya ce masa, “Ka yi mini wannan alheri, ka sa hannunka ƙarƙashin cinyar ƙafata, ka yi mini alkawari saboda ina roƙonka kaɗa ka bizne ni a Masar, 30 amma sa’ad da na huta da kakannina, ka ɗauke ni, ka fid da ni daga Masar, ka binne ni a inda aka binne su.”
Yusuf ya ce, “Zan yi yadda ka faɗa.”
31 Yaƙub ya ce, “Ka rantse mini.” Sai Yusuf ya rantse masa, Isra’ila kuwa ya yi godiya ga Allah yayinda ya jingina a kan sandansa.§
* 47:7 Ko kuwa gai da 47:10 Ko kuwa ya yi bankwana da 47:21 Fentatut da Seftuwajin (dubi kuma Bulget); Masoretik ya kai mutane zuwa birane. § 47:31 Ko kuwa Isra’ila ya rusuna a kan gadonsa