2
Gargaɗi don a mai da hankali
Dole mu ƙara mai da hankali sosai ga abubuwan da muka ji, don kada mu kauce. Gama in saƙon da aka faɗi ta bakin mala’iku ya zama tabbatacce, kuma kowane ƙeta umarni da rashin biyayya suka karɓi sakamakonsu da ya dace, yaya za mu tsira in muka ƙyale irin wannan babban ceto? Wannan ceto, wanda Ubangiji ne ya fara sanar, aka kuma tabbatar mana ta bakin waɗanda suka ji shi. Allah shi ma ya shaida ta wurin alamu, abubuwan banmamaki da mu’ujizai iri-iri, da kuma baye-bayen Ruhu Mai Tsarki da aka rarraba bisa ga nufinsa.
An yi Yesu kamar ’yan’uwansa
Ba ga mala’iku ba ne ya sa su yi mulkin duniya mai zuwa, wanda muke magana a kai ba. Amma akwai wani wurin da wani ya shaida cewa,
“Mene ne mutum, da kake tuna da shi,
ɗan mutum da kake kula da shi?
Ka sa shi ƙasa kaɗan da darajar mala’iku;
ka naɗa shi da ɗaukaka da girma,
ka kuma sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa.”*
Ta wurin sa kome a ƙarƙashinsa, Allah bai bar wani abu da bai sa a ƙarƙashinsa ba. Duk da haka a yanzu ba mu ga kowane abu a ƙarƙashinsa ba. Sai dai muna ganin Yesu, wanda aka mai da shi ƙasa kaɗan da darajar mala’iku, yanzu kuwa an naɗa shi da ɗaukaka da girma domin yă sha wahalar mutuwa, domin ta wurin alherin Allah yă ɗanɗana mutuwa saboda kowa.
10 Ta wurin kawo ’ya’ya masu yawa zuwa ga ɗaukaka, ya dace cewa Allah, wanda dominsa da kuma ta wurinsa ne kome yake kasancewa, ya sa tushen cetonsu yă zama cikakke ta wurin shan wahala. 11 Da shi wanda yake tsarkake mutane da kuma su waɗanda ake tsarkakewa duk ’yan iyali ɗaya ne. Saboda haka Yesu ba ya kunyan kiransu ’yan’uwansa. 12 Ya ce,
“Zan sanar da sunanka ga ’yan’uwana;
a gaban jama’a zan rera yabonka.”
13 Har wa yau ya ce,
“Zan dogara gare shi.”
Ya kuma ce,
“Ga ni, da ’ya’yan da Allah ya ba ni.”§
14 Da yake ’ya’yan suna da nama da jini, shi ma sai ya ɗauki kamanninsu na mutum domin ta wurin mutuwarsa yă hallaka wanda yake riƙe da ikon mutuwa, wato, Iblis 15 ya kuma ’yantar da waɗanda dukan rayuwarsu tsoron mutuwa ya riƙe su cikin bauta. 16 Gama tabbatacce ba mala’iku ne ya taimaka ba, sai dai zuriyar Ibrahim. 17 Saboda wannan dole a mai da shi kamar ’yan’uwansa ta kowace hanya, domin yă zama babban firist mai aminci da mai jinƙai cikin hidima ga Allah, yă kuma miƙa hadayar sulhu saboda zunuban mutane. 18 Domin shi kansa ya sha wahala sa’ad da aka gwada shi, yana iya taimakon waɗanda ake yi wa gwaji.
* 2:8 Zab 8.4-6 2:12 Zab 22.22 2:13 Ish 8.17 § 2:13 Ish 8.18