13
Fushin Ubangiji a kan Isra’ila
1 Sa’ad da Efraim ya yi magana, mutane sun yi rawan jiki;
an girmama shi a cikin Isra’ila.
Amma sai ya zama mai laifi na yin wa Ba’al sujada, ya kuwa mutu.
2 Yanzu sai yin zunubi a kai a kai suke;
suna yin gumaka wa kansu daga azurfansu,
da wayo suna sarrafa siffofi,
dukansu aikin masu aikin hannu ne.
Ana magana waɗannan mutane cewa,
“Suna miƙa hadayar mutum
su kuma sumbaci gumakan maruƙa.”
3 Saboda haka za su zama kamar hazon safiya,
kamar raɓar safen da yakan kakkaɓe,
kamar ƙaiƙayin da ake tankaɗe daga masussuka,
kamar hayaƙin da yake fita daga taga.
4 “Amma ni ne Ubangiji Allahnku,
wanda ya fitar da ku daga Masar.
Ba za ku yarda da wani Allah ba sai ni,
ba wani Mai Ceto in ban da ni.
5 Na lura da ku a hamada,
cikin ƙasar mai ƙunar zafi.
6 Sa’ad da na ciyar da su sun ƙoshi;
sa’ad da suka ƙoshi, sai suka fara taƙama;
sai suka manta da ni.
7 Saboda haka zan hau kansu kamar zaki,
zan ɓuya a bakin hanya kamar damisa.
8 Kamar beyar da aka ƙwace mata ’ya’yanta,
zan fāɗa musu in ɓarke su.
Kamar zaki zan cinye su;
kamar naman jeji zan yayyage su.
9 “An hallaka ku, ya Isra’ila,
domin kun tayar mini, kun tayar wa mai taimakonku.
10 Ina sarkinku, da zai cece ku?
Ina masu mulkinku cikin dukan garuruwanku,
waɗanda kuka ce,
‘Ba mu sarki da shugabanni’?
11 Saboda haka cikin fushina na ba ku sarki,
kuma cikin hasalata na ɗauke shi.
12 An yi ajiyar laifin Efraim,
aka lissafta zunubansa.
13 Naƙuda ta zo masa kamar a mace mai haihuwa,
amma shi yaro ne marar hikima;
sa’ad da lokaci ya kai,
ba ya zuwa inda mahaifa ta buɗe.
14 “Zan fanshe su daga ikon kabari;
zan cece su daga mutuwa.
Ina annobanki, ya mutuwa?
Ina hallakarka, ya kabari?
“Ba zan ji tausayi ba,
15 ko da ma ya ci gaba cikin ’yan’uwansa.
Iskar gabas daga Ubangiji za tă zo,
tana hurawa daga hamada;
maɓulɓularsa za tă kafe
rijiyarsa kuma ta bushe.
Za a kwashi kaya masu daraja
na ɗakin ajiyarsa ganima.
16 Dole mutanen Samariya su ɗauki laifinsu,
domin sun tayar wa Allahnsu.
Za a kashe su da takobi;
za a fyaɗa ƙananansu da ƙasa,
za a ɓarke matansu masu ciki.”