10
Kaiton waɗanda suke kafa dokokin rashin gaskiya,
waɗanda suke ba da ƙa’idodin danniya,
don su hana matalauta hakkinsu
su kuma ƙi yin shari’ar gaskiya a kan waɗanda suke zaluntar mutanena,
suna ƙwace wa gwauraye dukiyarsu
suna kuma yi wa marayu ƙwace.
Me za ku yi a ranan nan ta hukunci,
sa’ad da masifa ta zo daga nesa?
Ga wa za ku tafi don neman taimako?
Ina za ku bar dukiyarku?
Babu abin da zai rage sai cizon haƙora a cikin kamammu
ko mutuwa cikin waɗanda aka kashe.
 
Duk da haka, fushinsa bai huce ba,
hannunsa har yanzu yana a miƙe.
Hukuncin Allah a kan Assuriya
“Kaiton Assuriya, sandar fushina,
a hannun da kulkin fushina yake!
Na aike shi gāba da al’umma marar sanin Allah,
na tura shi gāba da mutanen da suka ba ni fushi,
don yă kwashe ganima yă kuma yi wason ganima,
yă tattake su kamar laka a tituna.
Amma ba abin da ya yi niyya ke nan ba,
ba abin da yake da shi a zuciya ba;
manufarsa shi ne yă hallaka,
yă kuma kawo ƙarshen al’ummai da yawa.
Ya ce, ‘Dukan shugabannin yaƙina ba sarakuna ba ne?’
‘Kalno bai kasance kamar Karkemish ba?
Hamat bai zama kamar Arfad
Samariya kuma kamar Damaskus ba?
10 Yadda hannuna ya ƙwace mulkokin gumaka,
mulkokin da siffofinsu suka fi na Urushalima da Samariya,
11 ba zan yi da Urushalima da siffofinta
yadda na yi da Samariya da gumakanta ba?’ ”
12 Sa’ad da Ubangiji ya gama dukan aikinsa gāba da Dutsen Sihiyona da Urushalima, zai ce, “Zan hukunta sarkin Assuriya saboda fariya na gangancin zuciyarsa da kuma kallon reni na idanunsa. 13 Gama ya ce,
“ ‘Ta wurin ƙarfin hannuna ne na aikata wannan,
da kuma ta wurin hikimata, gama ina da fahimi.
Na kau da iyakokin ƙasashe,
na washe dukiyarsu;
a matsayina na mai iko, na mamaye sarakunansu.
14 Kamar yadda mutum yakan miƙa hannu cikin sheƙar tsuntsu
haka hannuna ya je ya washe dukiyar al’ummai;
kamar yadda mutane sukan tattara ƙwai,
haka na tattara dukan ƙasashe;
ba tsuntsun da ya kakkaɓe fikafiki,
ko yă buɗe baki don yă yi kuka.’ ”
 
15 Gatari ya taɓa fin wanda yake amfani da shi girma,
ko zarto yă yi wa wanda yake amfani da shi taƙama?
Sanda za tă girgiza mutumin da yake riƙe da ita,
ko kuwa kulki yă jijjiga mutumin da yake riƙe da katako!
16 Saboda haka Ubangiji Maɗaukaki,
zai aukar da cuta mai kisa a kan ƙosassu jarumawa;
a ƙarƙashin sansaninsa zai ƙuna wuta
kamar harshen wuta.
17 Hasken Isra’ila zai zo kamar wuta,
Mai Tsarkinsu zai zama kamar wuta;
a rana guda zai ƙone yă kuma cinye
ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiyarsa.
18 Darajar jejinsa da gonakinsa masu dausayi
za a hallaka su ɗungum,
kamar yadda ciwo yakan kashe mutum.
19 Sauran itatuwan jejinsa kuma za su ragu
ko ɗan ƙaramin yaro ma zai iya ƙidaya su.
Raguwar Isra’ila
20 A wannan rana raguwar Isra’ila,
waɗanda suka ragu na gidan Yaƙub,
ba za su ƙara dogara ga
wanda ya kusa hallaka su ba
amma za su dogara ga Ubangiji,
Mai Tsarkin nan na Isra’ila.
21 Raguwa za tă komo,* raguwar Yaƙub
za su komo ga Maɗaukaki Allah.
22 Ko da yake mutanenka, ya Isra’ila, sun zama kamar yashin bakin teku,
raguwa ce kurum za tă komo.
A ƙaddara hallaka,
mai mamayewa da mai adalci.
23 Ubangiji Maɗaukaki, zai sa
hallakar da aka ƙaddara a kan dukan ƙasa ta faru.
24 Saboda haka, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce,
“Ya mutanena masu zama a Sihiyona,
kada ku ji tsoron Assuriyawa,
waɗanda suka dūke ku da sanda
suka kuma ɗaga kulki a kanku, kamar yadda Masar ta yi.
25 Ba da daɗewa ba fushina a kanku zai zo ga ƙarshe
hasalata kuma za tă koma ga hallakarsu.”
 
26 Ubangiji Maɗaukaki zai bulale su da tsumagiya,
kamar sa’ad da ya bugi Midiyan a dutsen Oreb;
zai kuma ɗaga sandarsa a bisa ruwaye,
yadda ya yi a Masar.
27 A wannan rana zai ɗauke nauyi daga kafaɗarku,
nauyinsu daga wuyanku;
za a karye karkiya
domin kun yi ƙiba ƙwarai.
 
28 Sun shiga Ayiyat;
sun bi ta Migron;
sun adana tanade-tanade a Mikmash.
29 Suka ƙetare ta hanya, suka kuma ce,
“Za mu kwana a Geba.”
Rama ta firgita;
Gibeya ta Shawulu ta gudu.
30 Ki yi ihu, ya Diyar Gallim!
Ki saurara, ya Layisha!
Kayya, Anatot abin tausayi!
31 Madmena tana gudu;
mutanen Gebim sun ɓuya.
32 A wannan rana za su dakata a Nob;
za su jijjiga ƙarfinsu
a dutsen Diyar Sihiyona,
a tudun Urushalima.
 
33 Duba, Ubangiji Maɗaukaki,
zai ragargaza rassa da iko mai girma.
Za a sassare itatuwa masu ganyaye,
za a yanke dogayen itatuwa har ƙasa.
34 Zai sassare itatuwan jeji da gatari har ƙasa;
Lebanon zai fāɗi a gaban Mai Iko.
* 10:21 Da Ibraniyanci sheyar-yashub; haka ma a aya 22.