13
Annabci a kan Babilon
Abubuwan da Allah ya yi magana a kai game da Babilon da Ishaya ɗan Amoz ya gani.
A tā da tuta a kan tudun da yake mai fili,
ka tā da murya gare su;
ka ɗaga hannu ka ba su alama
don su shiga ƙofofi masu alfarma.
Na umarci tsarkakana;
na umarci jarumawan yaƙina su gamsar da fushina,
waɗanda suke farin ciki a nasarata.
 
Ka saurara, akwai surutu a kan duwatsu,
sai ka ce na babban taron jama’a!
Ka saurara, akwai hayaniya a cikin mulkoki,
sai ka ce al’ummai ne suna ta tattaruwa!
Ubangiji Maɗaukaki yana shirya
mayaƙa don yaƙi.
Suna zuwa daga ƙasashe masu nesa,
daga iyakokin duniya,
Ubangiji da kuma fushinsa,
zai hallaka dukan ƙasar.
 
Ku yi ihu, gama ranar Ubangiji ta yi kusa
za tă zo kamar hallaka daga Maɗaukaki.*
Saboda wannan, hannun kowane mutum zai yi rauni,
ƙarfin halin kowane mutum zai kāsa.
Tsoro zai kama su,
zafi da azaba za su ci ƙarfinsu;
za su yi ta murɗewa kamar mace mai naƙuda.
Za su dubi juna a tsorace,
fuskokinsu a ɓace.
 
Duba, ranar Ubangiji tana zuwa,
muguwar rana, mai hasala da zafin fushi,
don ta mai da ƙasar kango
ta kuma hallakar da masu zunubi da suke cikinta.
10 Taurarin sama da ƙungiyoyinsu
ba za su ba da haskensu ba.
Rana za tă yi duhu
wata kuma ba zai ba da haskensa ba.
11 Zan hukunta duniya saboda muguntarta,
mugaye saboda zunubansu.
Zan kawo ƙarshe ga girman kan masu taƙama
in kuma ƙasƙantar da ɗaga kan marasa tausayi.
12 Zan sa mutum yă fi zinariya zalla wuyar samuwa,
fiye da zinariyar Ofir wuyan gani.
13 Saboda haka zan sa sammai su yi rawar jiki;
duniya kuma za tă girgiza daga inda take
a fushin Ubangiji Maɗaukaki,
a ranar fushinsa mai ƙuna.
 
14 Kamar barewar da ake farautarta
kamar tumaki marasa makiyayi,
haka nan kowane mutum zai koma ga mutanensa,
kowane mutum zai gudu zuwa ƙasarsa.
15 Duk wanda aka kama za a soke shi yă mutu;
dukan waɗanda aka kama za su mutu ta takobi.
16 Za a fyaɗa ’ya’yansu a ƙasa su yi kucu-kucu a idanunsu;
za a washe gidajensu, a kuma kwana da matansu.
 
17 Duba, zan zuga mutanen Medes su yi gāba da su,
su da ba su kula da azurfa ba
kuma ba sa damuwa da zinariya.
18 Bakkunansu za su kashe samari;
ba za su ji tausayin jarirai ba
ba za su kuwa nuna jinƙai ga ’yan yara ba.
19 Babilon, kayan daraja na mulkoki,
abin fariyar Babiloniyawa,
Allah zai kaɓantar da ita
kamar yadda ya yi da Sodom da Gomorra.
20 Ba za ƙara kasance da mazauna kuma ba
ko a yi zama a cikinta dukan zamanai;
Ba wani mutumin Arab da zai kafa tentinsa a can,
ba makiyayin da zai taɓa kiwon garkensa a can.
21 Amma halittun hamada za su kwanta a can,
diloli za su cika gidajenta;
a can mujiyoyi za su zauna,
a can kuma awakin jeji za su yi ta tsalle.
22 Kuraye za su yi ta kuka a kagarorinta,
diloli kuma a cikin fadodinta masu alfarma.
Lokacinta ya yi kusa,
kwanakinta kuma ba za su yi tsawo ba.
 
 
* 13:6 Da Ibraniyanci Shaddai 13:19 Ko kuwa Kaldiyawa