23
Annabci a kan Taya
1 Abin da Allah ya faɗa game da Taya.
Ku yi kuka mai zafi, ya jiragen ruwan Tarshish!
Gama an hallaka Taya
aka kuma bar su babu gida ko tasha.
Daga ƙasar Saifurus
magana ta zo musu.
2 Ku yi shiru, ku mutanen tsibiri
da ku ’yan kasuwan Sidon
waɗanda masu ciniki a teku suka azurta.
3 A manyan ruwaye
hatsin Shihor suka iso;
girbin Nilu ne kuɗin shiga na Taya
ta kuma zama kasuwar al’ummai.
4 Ki ji kunya, ya ke Sidon, da ke kuma, kagarar teku,
gama teku ya yi magana ya ce,
“Ban taɓa naƙuda ba balle in haifi ’ya’ya;
ban taɓa goyon ’ya’ya maza ba balle in reno ’ya’ya mata.”
5 Sa’ad da magana ta kai Masar,
za su razana da jin labari daga Taya.
6 Ku haye zuwa Tarshish;
ku yi kuka mai zafi, ku mutanen tsibiri.
7 Wannan ce birnin murnanku,
birnin nan na tun dā
wadda ƙafafunta suka kai ta
zama a ƙasashe masu nesa?
8 Wane ne ya ƙulla wannan a kan Taya
ita da take ba da rawanin sarauta,
wadda ’yan kasuwanta sarakuna ne,
wadda masu cinikinta sanannu ne a duniya?
9 Ubangiji Maɗaukaki ya ƙulla shi,
don yă kawo ƙarshen girman kan dukan darajarta
ya kuma ƙasƙantar da dukan waɗanda suke sanannu a duniya.
10 Ki nome ƙasarki har zuwa wajen Nilu,
Ya Diyar Tarshish,
gama ba ki da tashan jirgin ruwa kuma.
11 Ubangiji ya miƙa hannunsa a bisa teku
ya kuma sa mulkokinsa suka yi rawar jiki.
Ya ba da umarni game da Funisiya
cewa a hallaka kagararta.
12 Ya ce, “Ba za ki ƙara yin murna ba,
Ya ke Budurwa Diyar Sidon, yanzu da kike ragargajiya!
“Tashi, ki ƙetare zuwa Saifurus;
a can ɗin ma ba za ki huta ba.”
13 Dubi ƙasar Babiloniyawa,
wannan mutanen da yanzu ba su da wani amfani!
Assuriyawa sun mai da ita
wurin zaman halittun hamada;
sun gina hasumiyoyin kwanto,
suka ragargaza kagararta ƙaf
suka mai da ita kango.
14 Ku yi kuka mai zafi, ku jiragen ruwan Tarshish;
an rurrushe kagararku!
15 A wannan lokaci za a manta da Taya har shekaru saba’in, tsawon rayuwar sarki. Amma a ƙarshen waɗannan shekaru saba’in, zai zama wa Taya kamar yadda yake a waƙar karuwa cewa,
16 “Ɗauki garaya, ki ratsa birni,
Ya ke karuwar da aka manta da ita;
kaɗa garaya da kyau, ki rera waƙoƙi masu yawa,
saboda a tuna da ke.”
17 A ƙarshen shekaru saba’in, Ubangiji zai magance Taya. Za tă koma ga aikinta na karuwanci za tă kuma yi kasuwancinta da dukan mulkokin duniya.
18 Duk da haka za a keɓe ribarta da kuɗin shigarta wa Ubangiji; ba za a yi ajiyarsu ko a ɓoye su. Ribarta za tă tafi ga waɗanda suke yi wa Ubangiji sujada, don su sami yalwataccen abinci da tufafi masu kyau.