27
Ceton Isra’ila
A wannan rana,
Ubangiji zai yi hukunci da takobi,
takobinsa mai tsanani, mai ƙarfi da kuma mai muguwar ɓarna,
zai hukunta dodon ruwa macijin nan da ya kanannaɗe,
dodon ruwa macijin nan mai murɗewa;
zai kashe dodon nan na teku.
A wannan rana,
“Ku rera game da gonar inabi mai ba da ’ya’ya ku ce
Ni, Ubangiji na lura da ita;
na yi ta yin mata banruwa.
Na yi tsaronta dare da rana
don kada wani yă yi mata ɓarna.
Ban yi fushi ba.
Da a ce ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne suke kalubalanta na mana!
Zan fita in yi yaƙi da su;
da na sa musu wuta duka.
Ko kuma bari su zo wurina don mafaka;
bari su yi sulhu da ni,
I, bari su yi sulhu da ni.”
 
A kwanaki masu zuwa Yaƙub zai yi saiwa,
Isra’ila zai yi toho ya kuma yi fure
ya cika dukan duniya da ’ya’ya.
 
Ubangiji ya buge shi
kamar yadda ya bugi waɗanda suka buge shi?
An kashe shi
kamar yadda aka kashe waɗanda suka kashe shi?
Ta wurin yaƙi da zaman bauta ka hukunta shi,
da tsananin tsawa kuma ka kore shi,
kamar a ranar da iskar gabas ta hura.
A ta haka fa, za a yi kafarar laifin Yaƙub,
wannan kuma zai zama cikakken amfanin kau da zunubinsa.
Sa’ad da ya niƙa duwatsun bagade
suka zama kamar allin da aka farfashe kucu-kucu,
har ba sauran ginshiƙan Ashera ko bagadan ƙona turare
da za a bari a tsaye.
10 Birni mai katanga ya zama kufai,
yasasshen mazauni, an yashe shi kamar hamada;
a can ’yan maruƙa suke kiwo,
a can suke kwance;
sun kakkaɓe rassanta ƙaf.
11 Sa’ad da rassanta suka bushe, sai su kakkarye su
mata kuma su zo su yi itacen wuta da su.
Gama mutane ne marar azanci;
saboda haka Mahaliccinsu bai ji tausayinsu ba,
Mahaliccinsu bai nuna musu jinƙai ba.
12 A wannan rana Ubangiji zai tankaɗe daga Yuferites* mai gudu zuwa Rafin Masar, ku kuma, ya Isra’ilawa, za a tattara ku ɗaya-ɗaya. 13 Kuma a wannan rana zai busa ƙaho mai kāra sosai. Waɗanda suke mutuwa a Assuriya da kuma waɗanda aka kai zaman bauta a Masar za su zo su kuma yi wa Ubangiji sujada a dutse mai tsarki a Urushalima.
* 27:12 Da Ibraniyanci Kogi