34
Hukunci a kan al’ummai
Ku zo kusa, ku al’ummai, ku kuwa saurara
ku kasa kunne, ku mutane!
Bari duniya ta ji, da kuma dukan abin da yake cikinta,
duniya, da dukan abin da yake fitowa daga gare ta!
Ubangiji yana fushi da dukan al’ummai;
hasalarsa tana a kan mayaƙansu.
Zai hallaka su tas,
zai ba da su a karkashe.
Za a jefar da waɗanda aka kashe
gawawwakinsu za su yi wari;
duwatsu za su jiƙu da jininsu.
Za a tumɓuke dukan taurarin sammai
za a kuma nannaɗe sararin sama kamar littafi;
dukan rundunar sama za su fāffāɗi
kamar ganyayen da suka yanƙwane daga kuringa,
kamar ’ya’yan ɓauren da suka bushe daga itacen ɓaure.
Takobina ya sha zararsa a cikin sammai;
duba, ya sauko cikin hukunci a kan Edom,
mutanen da zan hallaka tas.
Takobin Ubangiji ya jiƙu da jini,
ya rufu da kitse,
jinin raguna da na awaki,
kitse daga ƙodar raguna.
Gama Ubangiji ya yi hadayar Bozra
da kuma babban kisa a Edom.
Babban bijimin jeji zai fāɗi tare da su,
maruƙan bijimi da manyan bijimai.
Ƙasarsu za tă cika da jini,
ƙura kuma zai cika da kitse.
 
Gama Ubangiji yana da ranar ɗaukar fansa,
shekarar ramuwa, don biya wa Sihiyona bukata.
Za a mai da rafuffukan Edom rami,
ƙurarta za tă zama kibiritun farar wuta;
ƙasarta za tă zama rami mai ƙuna!
10 Ba za a kashe ta ba dare da rana;
hayaƙinta za tă yi ta tashi har abada.
Daga tsara zuwa tsara za tă zama kango;
babu wani da zai ƙara wucewa ta wurin.
11 Mujiyar hamada da mujiya mai kuka za su mallake ta;
babban mujiya da hankaka za su yi sheƙa a can.
Allah zai miƙe a kan Edom
magwajin bala’i
da ma’aunin kango.
12 Sarakunanta ba za su kasance da wani abin da ake kira masarauta ba,
dukan sarakunanta za su ɓace.
13 Ƙayayuwa za su mamaye fadodinta
ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya za su cika kagaranta.
Za tă zama mazaunin diloli
da gida don mujiyoyi.
14 Halittun hamada za su sadu da kuraye,
awakin jeji za su yi ta kiran juna;
a can halittun dare su ma za su huta
su kuma nemi wurin hutu wa kansu.
15 Mujiya za tă yi sheƙa a can ta zuba ƙwai;
za tă ƙyanƙyashe su, ta kuma kula da ’ya’yanta a inuwar fikafikanta;
a can kuma shirwa za su taru,
kowa da abokinsa.
16 Duba a cikin littafin Ubangiji ka kuma karanta.
Babu wani a cikin waɗannan da ya ɓace,
babu ko ɗaya da ba ta da abokiya.
Gama bakinsa ne ya ba da umarni,
Ruhunsa kuma zai tara su wuri ɗaya.
17 Ya ba su rabonsu;
hannunsa ya rarraba musu ta wurin awo.
Za su mallake ta har abada
su kuma zauna a can daga tsara zuwa tsara.