40
Ta’aziyya don mutanen Allah
Ta’aziyya, ku ta’azantu mutanena,
in ji Allahnku.
Yi magana mai kwantar da rai ga Urushalima,
ku kuma furta mata
cewa aiki mai zafinta ya isa,
cewa an fanshi zunubinta,
cewa ta karɓi daga hannun Ubangiji
ninki biyu saboda dukan zunubanta.
 
Muryar wani tana kira cewa,
“A cikin hamada ku shirya
hanya saboda Ubangiji;*
ku miƙe manyan hanyoyi domin Allahnmu
a cikin jeji.
Za a cike kowane kwari,
a baje kowane dutse da kowane tudu;
za a mayar da karkatattun wurare su zama sumul,
munanan wurare kuma su zama da kyau.
Za a kuma bayyana ɗaukakar Ubangiji,
dukan mutane kuwa za su gan ta.
Gama Ubangiji da kansa ne ya yi magana.”
 
Muryar tana cewa, “Ka yi shela.”
Na kuwa ce, “Me zan yi shelar?”
 
“Dukan mutane kamar ciyawa suke,
kuma dukan ɗaukakarsu kamar furannin jeji ne.
Ciyawa takan yanƙwane, furanni kuma su yi yaushi,
domin Ubangiji ya hura iska a kansu.
Tabbatacce mutane ciyawa ne.
Hakika ciyawa takan yanƙwane, furanni kuma su yi yaushi,
amma maganar Allahnmu tana nan daram har abada.”
 
Kai da ka kawo labari mai daɗi wa Sihiyona,
ka haura a bisa dutse.
Kai da ka kawo labari mai daɗi wa Urushalima,
ka tā da muryarka ka yi ihu,
ka ɗaga ta, kada ka ji tsoro;
faɗa wa garuruwan Yahuda,
“Ga Allahnku!”
10 Duba, Ubangiji Mai Iko Duka yana zuwa da iko,
hannunsa kuma yana yin mulki dominsa.
Duba, ladarsa tana tare da shi,
sakamakonsa kuma na rakiyarsa.
11 Yakan lura da garkensa kamar makiyayi.
Yakan tattara tumaki wuri ɗaya
yă riƙe su kurkusa da ƙirjinsa;
a hankali kuma yakan bi da masu ba da mama.
 
12 Wane ne ya auna ruwaye a tafin hannunsa,
ko kuwa ya gwada tsawon sammai da fāɗin tafin hannunsa?
Wane ne ya riƙe ƙurar ƙasa a kwando,
ko kuwa ya auna nauyin duwatsu a magwaji,
tuddai kuma a ma’auni?
13 Wane ne ya fahimci zuciyarUbangiji,
ko kuwa ya koya masa a matsayin mashawarcinsa?
14 Wane ne Ubangiji ya nemi shawararsa don yă ganar da shi,
wane ne kuma ya koya masa hanyar da ta dace?
Wane ne ya koya masa sani
ko ya nuna masa hanyar fahimta?
 
15 Tabbatacce al’ummai suna kama da ɗigon ruwa a cikin bokiti
an ɗauke su a matsayin ƙura a kan magwaji;
yakan auna tsibirai sai ka ce ƙura mai laushi.
16 Itatuwan Lebanon ba su isa a yi wutar bagade da su ba,
balle dabbobinsa su isa yin hadayun ƙonawa.
17 A gabansa dukan al’ummai ba kome ba ne;
ya ɗauke su ba a bakin kome ba
kuma banza ne kurum.
 
18 To, ga wane ne za ka kwatanta Allah?
Wace siffa za ka kwatanta shi da ita?
19 Gunki dai, maƙeri kan yi zubinsa,
maƙerin zinariya kuma yă ƙera shi da zinariya
yă kuma sarrafa masa sarƙoƙin azurfa.
20 Mutumin da talauci ya sha kansa da ba zai iya miƙa irin hadayar nan ba
kan zaɓi itacen da ba zai ruɓe ba.
Yakan nemi gwanin sassaƙa
don yă sassaƙa masa gunkin da ba zai fāɗi ba.
 
21 Ba ku sani ba?
Ba ku taɓa ji ba?
Ba a faɗa muku daga farko ba?
Ba ku fahimta ba tun kafawar duniya?
22 Yana zaune a kursiyi a bisa iyakar duniya,
kuma mutanenta suna kama da fāra.
Ya miƙa sammai kamar rumfa,
ya kuma shimfiɗa su kamar tentin da za a zauna a ciki.
23 Yakan mai da sarakuna ba kome ba
yă mai da masu mulkin wannan duniya wofi.
24 Ba da jimawa ba bayan an shuka su,
ba da jimawa ba bayan an dasa su,
ba da jimawa ba bayan sun yi saiwa a ƙasa,
sai yă hura musu iska su yanƙwane,
guguwa kuma ta kwashe su kamar yayi.
 
25 “Ga wa za ku kwatanta ni?
Ko kuwa wa yake daidai da ni?” In ji Mai Tsarkin nan.
26 Ku ɗaga idanunku ku duba sammai.
Wane ne ya halicce dukan waɗannan?
Wane ne ya fitar da rundunar taurari ɗaya-ɗaya,
yana kiransu, kowanne da sunansa.
Saboda ikonsa mai girma da kuma ƙarfinsa mai girma,
babu ko ɗayansu da ya ɓace.
 
27 Ya Yaƙub, ya Isra’ila, me ya sa kake ce
kana kuma gunaguni cewa,
“Hanyata tana a ɓoye daga Ubangiji;
Allah bai kula da abin da yake damuna ba”?
28 Ba ku sani ba?
Ba ku ji ba?
Ubangiji madawwamin Allah ne,
Mahaliccin iyakokin duniya.
Ba zai taɓa gaji ko yă kasala ba,
kuma fahimtarsa ya wuce gaban ganewar mutum.
29 Yakan ba da ƙarfi ga waɗanda suka gaji
yă kuma ƙara ƙarfi ga marasa ƙarfi.
30 Ko matasa ma kan gaji su kuma kasala,
samari kuma kan yi tuntuɓe su fāɗi;
31 amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji
za su sabunta ƙarfinsu.
Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa;
za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba,
za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.
* 40:3 Ko kuwa Muryar wani mai kira a cikin hamada. “Ku shirya hanya domin Ubangiji”. 40:9 Ko kuwa Ya Sihiyona, mai kawo labari mai daɗi, haura bisa dutse. Ya Urushalima, mai kawo labari mai daɗi 40:13 Ko kuwa Ruhun; Ko kuwa ruhu