10
“Na gaji da rayuwa;
saboda haka bari in faɗi zuciyata gabagadi
yadda raina yake jin ba daɗi.
Zan ce wa Allah, kada ka hukunta ni,
amma ka gaya mini laifin da na yi maka.
Kana jin daɗin ba ni wahala,
don me ka yashe ni, abin da ka halitta da hannunka,
yayinda kake murmushi game da shirye-shiryen mugaye?
Idanunka irin na mutum ne?
Kana gani yadda mutum yake gani ne?
Kwanakinka kamar na mutane ne,
ko shekarunka kamar na mutane ne
da za ka neme ni da laifi
ka hukunta ni?
Ko da yake ka san ba ni da laifi,
kuma ba wanda zai iya cetona daga hannunka.
 
“Da hannuwanka ka ƙera ni, kai ka halicce ni.
Yanzu kuma kai za ka juya ka hallaka ni?
Ka tuna cewa ka mulmula ni kamar yumɓu.
Yanzu za ka mai da ni in zama ƙura kuma?
10 Ba kai ka zuba ni kamar madara ba,
na daskare kamar cuku.
11 Ka rufe ni da tsoka da fata,
ka harhaɗa ni da ƙasusuwa da jijiyoyi?
12 Ka ba ni rai ka kuma yi mini alheri,
kuma cikin tanadinka ka kula da ruhuna.
 
13 “Amma wannan shi ne abin da ka ɓoye a zuciyarka,
na kuma san abin da yake cikin zuciyarka ke nan.
14 In na yi zunubi kana kallo na
kuma ba za ka fasa ba ni horo ba don laifin da na yi.
15 Idan ina da laifi, kaitona!
Ko da ba ni da laifi, ba zan iya ɗaga fuskata ba,
gama kunya ta ishe ni
duk ɓacin rai ya ishe ni.
16 In na ɗaga kaina, za ka neme ni kamar zaki
ka sāke nuna al’ajabin ikonka a kaina.
17 Kana sāke kawo sababbin waɗanda za su ba da shaida a kaina
kana ƙara haushinka a kaina;
kana ƙara kawo mini hari.
 
18 “Me ya sa ka fito da ni daga cikin uwata?
Da ma na mutu kafin a haife ni.
19 Da ma ba a halicce ni ba,
da na mutu tun daga cikin cikin uwata na wuce zuwa kabari!
20 ’Yan kwanakina ba su kusa ƙarewa ba ne?
Ka rabu da ni don in ɗan samu sukuni na ɗan lokaci
21 kafin in koma inda na fito,
ƙasa mai duhu da inuwa sosai,
22 zuwa ƙasa mai duhun gaske,
da inuwa da hargitsi,
inda haske yake kamar duhu.”