26
Ayuba
Sai Ayuba ya amsa,
“Yadda ka taimaki marar ƙarfi!
Yadda ka ceci marar ƙarfi!
Ka ba marar hikima shawara!
Ka nuna kana da ilimi sosai.
Wane ne ya taimake ka ka yi waɗannan maganganu?
Kuma ruhun wane ne ya yi magana ta bakinka?
 
“Matattu suna cikin azaba, waɗanda suke ƙarƙashin ruwaye
da dukan mazauna cikin ruwaye.
Mutuwa tsirara take a gaban Allah;
haka kuma hallaka take a buɗe.
Ya shimfiɗa arewancin sararin sama a sarari;
ya rataye duniya ba a jikin wani abu ba.
Ya naɗe ruwaye a cikin gizagizansa,
duk da haka girgijen bai yage saboda nauyi ba.
Ya rufe fuskar wata,
ya shimfiɗa gizagizai a kan shi,
10 ya zāna iyakar fuskar ruwa
a kan iyakar da take tsakanin duhu da haske.
11 Madogaran sama sun girgiza,
saboda tsawatawarsa.
12 Da ikonsa ya kwantar da teku;
da hikimarsa ya hallaka dodon ruwan nan Rahab.
13 Da numfashinsa ya sa sararin sama ya yi kyau
da hannunsa ya soke macijin nan mai gudu.
14 Waɗannan kaɗan ke nan daga cikin ayyukansa masu yawa.
Kaɗan kawai muke ji game da shi!
Wane ne kuwa yake iya gane tsawar ikonsa?”