34
Sa’an nan Elihu ya ce,
“Ku ji maganata, ku masu hikima;
ku saurare ni, ku masu ilimi.
Gama kunne yana rarrabe magana
kamar yadda harshe yake ɗanɗana abinci.
Bari mu zaɓi abin da yake daidai,
bari mu koyi abin da yake mai kyau tare.
 
“Ayuba ya ce, ‘Ba ni da laifi,
amma Allah ya hana mini hakkina.
Ko da yake ina da gaskiya,
an ɗauke ni maƙaryaci;
ko da yake ba ni da laifi,
kibiyoyinsa sun ji mini ciwo wanda ba ya warkewa.’
Wane mutum ne kamar Ayuba,
wanda yake shan ba’a kamar ruwa?
Yana abokantaka da masu aikata mugunta;
yana cuɗanya da mugaye.
Gama ya ce, ‘Ba ribar da mutum zai samu
lokacin da yake ƙoƙari yă faranta wa Allah zuciya.’
 
10 “Saboda haka ku saurare ni, ku masu ganewa.
Ko kaɗan Allah ba ya mugunta,
Maɗaukaki ba ya kuskure.
11 Yana biyan mutum bisa ga abin da ya yi;
yana kawo masa abin da ayyukansa suka jawo.
12 Ba zai yiwu Allah yă yi ba daidai ba,
Maɗaukaki ba zai yi shari’a marar gaskiya ba.
13 Wane ne ya ba shi iko yă lura da duniya?
Wane ne ya ba shi iko kan dukan duniya?
14 In nufinsa ne
ya kuma janye ruhunsa da numfashinsa,
15 ’yan adam duka za su hallaka tare,
mutum kuma zai koma ƙasa.
 
16 “In kana da ganewa sai ka saurari wannan;
ka saurari abin da zan ce.
17 Maƙiyin gaskiya zai iya yin mulki?
Za ka iya ba mai gaskiya, Maɗaukaki laifi?
18 Ba shi ne ya ce wa sarakuna, ‘Ba ku da amfani ba,’
ya ce wa manya ‘Ku mugaye ne,’
19 wanda ba ya nuna sonkai ga ’ya’yan sarki
kuma ba ya goyon bayan masu arziki a kan matalauta,
gama dukansu shi ya yi su da hannuwansa.
20 Suna mutuwa nan take, a cikin tsakiyar dare;
an girgiza mutanen amma sun wuce;
an taɓa manya amma ba da hannun mutum ba.
 
21 “Idanunsa suna kan al’amuran mutane;
yana ganin tafiyarsu duka.
22 Babu wuri mai duhu, babu inuwa mai duhu,
inda masu aikata mugunta za su ɓoye.
23 Allah ba ya bukata yă ci gaba da bincike mutane,
har da za su zo gabansa don yă shari’anta su.
24 Ba tare da tambaya ba yana ragargaza masu iko,
yă kuma sa waɗansu a wurinsu.
25 Gama yana sane da abubuwan da suke yi,
yana hamɓarar da su da dare a kuma ragargaza su.
26 Yana ba su horo, don muguntarsu,
inda kowa zai gan su,
27 domin sun juya daga binsa,
kuma ba su kula da hanyoyinsa ba.
28 Sun sa kukan matalauta ya kai wurinsa
yadda ya kai ga jin kukan masu bukata.
29 Amma in ya yi shiru, wa zai ba shi laifi?
In ya ɓoye fuskarsa, wa zai gan shi?
Duk da haka shi yake da iko kan mutum da al’umma duka,
30 yana hana wanda bai san Allah ba yă yi mulki,
ya hana shi sa wa mutane tarko.
 
31 “A ce mutum ya ce wa Allah, ‘Na yi laifi,
amma ba zan sāke saɓa wa wani ba.
32 Ka koya mini abin da ba zan iya gani ba;
in na yi ba daidai ba, ba zan sāke yi ba.’
33 Ya kamata Allah yă yi maka bisa ga abin da ka ce ne,
sa’ad da ka ƙi ka tuba?
Dole kai ka zaɓa, ba ni ba;
yanzu ka gaya mini abin da ka sani.
 
34 “Mutane masu ganewa za su ce,
masu hikima waɗanda suka ji ni za su ce mini,
35 ‘Ayuba ya yi magana cikin rashin sani;
maganganunsa na marar hikima ne.’
36 Kash, da za a gwada Ayuba har ƙarshe,
domin yana ba da amsa kamar mugun mutum.
37 Ya ƙara tawaye a kan zunubansa;
ya tafa hannuwansa na reni a cikinmu
ya kuma ƙara yawan maganganunsa ga Allah.”