7
“Mutum bai sha wahalar aiki ba a duniya?
Rayuwarsa ba kamar ta wanda aka yi hayarsa ba ne?
Kamar yadda bawa yakan jira yamma ta yi,
ko kuma kamar yadda wanda aka yi hayarsa yakan jira a biya shi kuɗin aikin da ya yi.
Saboda haka rabona shi ne watanni na zama banza,
kowane dare kuwa sai ɓacin rai nake samu.
Lokacin da na kwanta ina tunani, ‘Har sai yaushe zan tashi?’
Gari ya ƙi wayewa, ina ta jujjuyawa har safe.
Jikina duk tsutsotsi da ƙuraje sun rufe shi,
fatar jikina ta ruɓe tana fitar da ruwan miki.
 
“Kwanakina suna wucewa da sauri, fiye da yadda ƙoshiyar masaƙa take wucewa da sauri,
za su kawo ga ƙarshe ba bege.
Ka tuna, ya Allah, raina numfashi ne kawai;
idanuna ba za su taɓa sāke ganin farin ciki ba.
Idanun da suke ganina yanzu ba za su sāke ganina ba;
za ku neme ni amma ba za ku same ni ba.
Kamar yadda girgije yakan ɓace yă tafi,
haka mutum yake shige zuwa kabari ba kuwa zai dawo ba.
10 Ba zai taɓa zuwa gidansa ba;
ba za a sāke san da shi ba.
 
11 “Saboda haka ba zan yi shiru ba;
zan yi magana cikin ɓacin raina,
zan nuna ɓacin raina cikin ruhu, cikin ƙuncin raina.
12 Ni teku ne, ko kuwa dodon ruwa,
don me kake tsaro na?
13 Lokacin da nake zato zan sami salama
in na kwanta a gadona don in huta,
14 duk da haka kana ba ni tsoro da mafarke-mafarke,
kana tsorata ni da wahayi.
15 Na gwammace a shaƙe ni in mutu
maimakon in kasance cikin wannan jiki.
16 Ba na so in zauna da rai; ba zan rayu ba har abada.
Ku rabu da ni; rayuwata ba ta da amfani.
 
17 “Mene ne mutum har da ka kula da shi haka,
har ka mai da hankali a kansa,
18 har kake duba shi kowace safiya,
kake kuma gwada shi koyaushe?
19 Ba za ka ɗan daina kallo na ba
ko ka rabu da ni na ɗan lokaci?
20 In na yi zunubi, me na yi maka,
kai mai lura da mutane?
Don me ka sa ni a gaba?
Na zame maka kaya mai nauyi ne?
21 Me ya sa ba za ka gafarta mini laifofina ba?
Gama na kusa kwantawa cikin ƙasa;
za ka neme ni,
amma ba za ka same ni ba.”