19
Balawe da ƙwarƙwararsa
A kwanakin nan Isra’ila ba su da sarki.
To, wani Balawe wanda yake zama a wani lungu na ƙasar tudu ta Efraim ya ɗauko wa kansa ƙwarƙwara daga Betlehem cikin Yahuda. Amma ba tă yi aminci ba. Ta bar shi ta komo gidan mahaifiyarta a Betlehem, a Yahuda. Bayan ta zauna a can wajen wata huɗu, sai mijinta ya je wajenta biko don yă rarashe ta komo. Ya tafi tare bawansa da kuma jakuna biyu. Sai ta shigar da shi gidan mahaifinta, sa’ad da mahaifinta ya gan shi, ya marabce shi da murna. Surukinsa, mahaifin yarinyar, ya sha kansa, yă dakata; saboda haka ya dakata tare da shi har kwana uku, yana ci yana sha, yana kuma kwanciya a can.
A rana ta huɗu suka tashi da sassafe ya kuma yi shiri yă tafi, amma mahaifinta yarinyar ya ce wa surukinsa, “Ka ɗan ci wani abu don ka sami ƙarfi; sa’an nan ka tafi.” Saboda haka suka zauna su biyu suka ci suka sha tare. Bayan haka sai mahaifin yarinyar ya ce, “Don Allah ka kwana ka ji wa kanka daɗi.” Sa’ad da mutumin ya tashi zai tafi, sai surukinsa ya roƙe shi, saboda haka ya kwana a wannan dare. Da sassafen kashegari rana ta biyar, ya tashi zai tafi, sai mahaifin yarinyar ya ce, “Ka ɗan zauna ka shaƙata sai rana ta yi sanyi mana!” Saboda haka su biyu suka zauna suka ci abinci tare.
Sa’ad da mutumin da ƙwarƙwaransa da bawansa, suka tashi don su tafi, surukinsa, mahaifin yarinyar ya ce, “Duba, rana ta kusan fāɗuwa, yamma ta riga ta yi, ka kwana a nan. Ka sāke kwana ka ji wa ranka daɗi. Kashegari da sassafe za ka iya tashi ka kama hanyarka zuwa gida.” 10 Amma bai so ya sāke kwana a can ba, mutumin ya tashi ya tafi ya bi ta Yebus (wato, Urushalima), tare da jakunansa biyu da aka yi musu shimfiɗa da kuma ƙwarƙwaransa.
11 Sa’ad da suka yi kusa da Yebus dare kuma ya riga ya yi, bawan ya ce wa maigidansa, “Mu dakata a birnin nan na Yebusiyawa mu kwana.”
12 Maigidansa ya ce, “A’a. Ba za mu shiga birnin baƙi waɗanda mutanensu ba Isra’ilawa ba. Za mu ci gaba zuwa Gibeya.” 13 Ya kuma ce, “Zo, mu yi ƙoƙari mu kai Gibeya ko Rama mu kwana a ɗaya cikinsu.” 14 Saboda haka suka ci gaba, rana tana fāɗuwa sa’ad da suka yi kusa da Gibeya a Benyamin. 15 A can suka dakata don su kwana, suka tafi suka zauna a dandali birnin, amma wani ya shigar da su gidansa da daren.
16 A wannan yamma sai ga wani tsoho daga ƙasar tudu ta Efraim, wanda yake zama a Gibeya (mutane wurin kuwa mutanen Benyamin ne), ya shigo daga wurin aiki a gonaki. 17 Sa’ad da ya duba ya ga matafiyin a dandalin birnin, sai tsohon ya yi tambaya ya ce, “Ina za ku? Ina kuka fito?”
18 Balawen ya ce, “Muna fito daga Betlehem a Yahuda za mu wani lungu a ƙasar tudu ta Efraim inda nake da zama. Na tafi Betlehem a Yahuda, ga shi kuwa yanzu za ni gidan Ubangiji. Ba wanda ya shigar da ni gidansa. 19 Muna da ƙara da abinci don jakunanmu, muna kuma da burodi da ruwan inabi dominmu da bayinka, ni, baiwarka da kuma saurayin nan tare da mu. Ba ma bukatar kome.”
20 Tsohon ya ce, “Na marabce ku a gidana. Bari ni ba ku duk abin da kuke bukata. Kada ku dai kwana a dandali.” 21 Saboda haka sai kai shi zuwa gidansa ya ciyar da jakunansa. Bayan sun wanke ƙafafunsu, sai aka ba su abinci da abin sha.
22 Yayinda suke jin wa kansu daɗi, sai waɗansu ’yan iska daga birnin suka kewaye gidan. Suna bubbuga ƙofar, suna kira tsohon da yake da gidan suna cewa, “Ka fito mana da mutumin nan a gidanka domin mu yi jima’i da shi.”
23 Maigidan ya fita waje ya ce musu, “A’a, abokaina, kada ku yi abin kunyan nan. Da yake mutumin nan baƙona ne, kada ku yi rashin kunyan nan. 24 Duba, ga ’yata da ba tă taɓa sanin namiji ba da kuma ƙwarƙwaransa. Zan fito muku da su a waje yanzu, za ku kuwa iya yin ko mene ne da kuke so da su. Amma wannan mutum, kada ku yi abin kunya.”
25 Amma mutanen ba su saurare shi ba. Saboda haka mutumin ya ba da ƙwarƙwaransa, suka yi mata fyaɗe suka yi lalata da ita dukan dare, gari yana wayewa sai suka bar ta. 26 Da safe matar ta koma gidan da maigidanta yake, ta fāɗi a ƙofa ta kwanta a can har rana ta yi.
27 Sa’ad da maigidanta ya tashi da safe ya buɗe ƙofar gidan don yă fita ya ci gaba da tafiyarsa, sai ga ƙwarƙwararsa, ta fāɗi a bakin ƙofar gidan da hannuwanta a madogarar ƙofar. 28 Ya ce mata, “Tashi; mu tafi.” Amma ba amsa. Sai ya sa ta a kan jakinsa ya kama hanyar gida.
29 Da ya kai gida, sai ya ɗauki wuƙa ya yayyanka ƙwarƙwaransa gunduwa-gunduwa, kashi goma sha biyu ya aika da su a ko’ina a Isra’ila. 30 Duk wanda ya gani, sai ya ce, “Ba a taɓa gani ko yin irin wannan abu ba, tun lokacin da Isra’ilawa suka fito daga Masar. Ku yi tunani wannan! Ku kuma yi la’akari! Ku gaya mana abin da za mu yi!”