14
Fari, yunwa da takobi
1 Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya game da fări cewa,
2 “Yahuda tana makoki
biranenta suna fama;
suna kuka saboda ƙasar,
kuka kuma tana tasowa daga Urushalima.
3 Manyan mutane suna aika bayinsu su ɗebo ruwa
a maɓulɓulai amma babu ruwa.
Suka dawo da tulunansu haka nan;
da kunya da kuma ƙasƙanci, da kawunansu a rufe.
4 Ƙasa ta tsattsage
saboda babu ruwan sama a ƙasar;
manoma sun sha kunya
suka kuma rufe kawunansu.
5 Har barewa a kurmi ma
ta gudu ta bar ’ya’yan da ta haihu sababbi
saboda babu ciyawa.
6 Jakan jeji suna tsaye a kan tuddai
suna haki kamar diloli;
idanunsu sun kāsa gani
saboda rashin makiyaya.”
7 Ko da yake zunubanmu suna ba da shaida a kanmu,
Ya Ubangiji, ka yi wani abu saboda sunanka.
Gama jan bayanmu ya yi yawa;
mun yi maka zunubi.
8 Ya kai, Sa Zuciyar Isra’ila,
Mai Cetonsa a lokutan wahala,
me ya sa kake yi kamar baƙo a ƙasar,
kamar matafiyi wanda yake shirya wuri don yă kwana gari ya waye ya wuce?
9 Me ya sa kake yi kamar mutumin da aka far masa kwasam ba zato,
kamar jarumi marar ƙarfin ceto?
Kana a cikinmu, ya Ubangiji,
da sunanka ake kiranmu;
kada ka yashe mu!
10 Ga abin da Ubangiji ya ce game da wannan mutane,
“Suna son yawace-yawace ƙwarai;
ba sa hana ƙafafunsu yawo.
Saboda haka Ubangiji bai yarda da su ba;
yanzu zai tuna da muguntarsu
zai kuma hukunta su saboda zunubansu.”
11 Sa’an nan Ubangiji ya ce mini, “Kada ka yi addu’a domin zaman lafiyar mutanen nan.
12 Ko da yake suna azumi, ba zan saurari kukansu ba, ko da yake suna miƙa hadayun ƙonawa da hadayun gari, ba zan yarda da su ba. A maimako zan hallaka su da takobi, yunwa da annoba.”
13 Amma na ce, “A, Ubangiji Mai Iko Duka, annabawa sun riƙa ce musu, ‘Ba za ku ga takobi ko ku yi fama da yunwa ba. A maimako, zan ba ku madawwamiyar salama.’ ”
14 Sai Ubangiji ya ce mini, “Annabawa suna ta annabcin ƙarya da sunana. Ban aike su ba, ban kuma naɗa su ba, ban yi musu magana ba. Suna muku annabci wahayin ƙarya, suna muku duba marar amfani, suna bautar gumaka suna kuma bayyana tunanin kansu ne.
15 Saboda haka, ga abin da Ubangiji ya ce game da annabawan da suke annabci da sunana. Ban aike su ba, duk da haka suna cewa, ‘Babu takobi ko yunwar da zai taɓa wannan ƙasa.’ Waɗannan annabawa takobi da yunwa za su hallaka su.
16 Mutanen da suke musu annabcin kuwa za a kore su zuwa titunan Urushalima saboda yunwa da kuma takobi. Babu wanda zai binne su, ko ya binne matansu, ko ’ya’yansu maza da mata. Zan aukar musu da masifar da ya dace da su.
17 “Ka yi musu wannan magana,
“ ‘Bari idanuna su yi ta zub da hawaye
dare da rana kada su daina;
saboda ’yata budurwa, mutanena,
sun sha wahalar babban rauni,
an yi musu bugu mai ragargazawa.
18 In na shiga cikin ƙasar,
na ga waɗanda takobi ya kashe;
in na shiga cikin birni,
na ga waɗanda suke fama da yunwa.
Da Annabi da firist duk
sun tafi ƙasar da ba su sani ba.’ ”
19 Ka ƙi Yahuda ɗungum ke nan?
Kana ƙyamar Sihiyona ne?
Me ya sa ka buge mu
don kada mu warke?
Mun sa zuciya ga salama
babu abin alherin da ya zo,
mun sa rai ga lokacin warkarwa
amma sai ga razana.
20 Ya Ubangiji, mun gane da muguntarmu
da kuma laifin kakanninmu;
tabbatacce mun yi maka zunubi.
21 Saboda sunanka kada ka ƙi mu;
kada ka ƙasƙantar da kursiyoyinka mai ɗaukaka.
Ka tuna da alkawarinka da mu
kada ka tā da shi.
22 Akwai wani daga cikin gumaka marasa amfani na al’ummai da ya kawo ruwan sama?
Sararin sama kansu sukan yi yayyafi?
A’a, kai ne, ya Ubangiji Allahnmu.
Saboda haka sa zuciyarmu tana a kanka,
gama kai ne kake yi wannan duka.