19
Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Tafi ka sayo tulu a wurin mai ginin tukwane. Ka ɗauki waɗansu dattawan jama’a da kuma na firistoci ku fita zuwa Kwarin Ben Hinnom, kusa da mashigin Ƙofar Kasko. A can ka furta maganganun da na faɗa maka, ka ce, ‘Ku ji maganar Ubangiji, ya sarakunan Yahuda da kuma mutanen Urushalima. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ku saurara! Zan kawo masifa a wannan wuri, wanda duk ya ji, kunnuwansa za su kaɗa. Gama sun yashe ni suka kuma mai da wannan wuri ya zama na baƙin alloli; sun ƙone hadayu a cikinsa wa allolin da ko su ko kakanninsu ko sarakunan Yahuda ba su taɓa sani ba, suka kuma cika wannan wuri da jini marasa laifi. Suka gina masujadai na kan tudu na Ba’al don su ƙona ’ya’yansu maza a cikin wuta a matsayin hadaya ga Ba’al abin da ban umarta ba, ban ambata ba, bai kuma zo mini ba. Saboda haka ku lura, kwanaki suna zuwa, in ji Ubangiji, sa’ad da mutane ba za su ƙara ce da wannan wuri Tofet ko Kwarin Ben Hinnom ba, amma za su ce da shi Kwarin Kisa.
“ ‘A wannan wuri zan lalace* dabarun Yahuda da na Urushalima. Zan sa a kashe su da takobi a gaban abokan gābansu, a hannuwan waɗanda suke neman ransu, zan kuma ba da gawawwakinsu su zama abinci ga tsuntsayen sararin sama da kuma namun jeji. Zan ragargazar da wannan birni in mai da shi abin reni, duk wanda ya wuce zai yi mamaki ya kuma yi tsaki saboda dukan masifunsa. Zan sa su ci naman ’ya’yansu maza da mata, za su kuma ci naman juna a lokacin damuwar ƙawanya da abokan gāban da suke neman ransu za su yi musu.’
10 “Sa’an nan ka fasa tulun yayinda waɗanda suka tafi tare da kai suna duba, 11 ka kuma ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa zan farfasa wannan al’umma da wannan birni kamar yadda aka farfasa wannan tulu mai ginin tukwane ba kuwa zai gyaru ba. Za a binne matattu a Tofet har sai ba sauran wuri. 12 Ga abin da zan yi wa wannan wuri da waɗanda suke zaune a nan, in ji Ubangiji. Zan mai da wannan birni kamar Tofet. 13 Gidaje a Urushalima da waɗannan na sarakunan Yahuda za su ƙazantu kamar wannan wuri, Tofet, dukan gidajen da suke ƙone turare a kan rufi wa duk rundunan taurari suna kuma zuba hadayun sha ga sauran alloli.’ ”
14 Sa’an nan Irmiya ya komo daga Tofet, inda Ubangiji ya aike shi don yă yi annabci, ya tsaya a filin haikalin Ubangiji ya ce wa mutane duka, 15 “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Ku saurara! Zan kawo wa wannan birni da ƙauyukan da suke kewayensa kowace masifar da na furta a kansu, domin sun yi taurinkai, ba su kuwa saurari maganata ba.’ ”
* 19:7 Ibraniyanci na lalace ya yi kamar Ibraniyanci na tulu (dubi ayoyi 1 da 10).