5
Ba ko ɗaya da yake da adalci
1 “Ku yi ta kai da kawowa a titunan Urushalima,
ku dudduba ko’ina ku kuma lura,
ku bincika cikin dandalinta.
Ko za ku sami mutum guda
wanda yake aikata adalci wanda yake kuma son bin gaskiya,
sai in gafarta wa wannan birni.
2 Ko da yake suna cewa, ‘Muddin Ubangiji yana raye,’
duk da haka suna rantsuwar ƙarya.”
3 Ya Ubangiji, idanunka ba sa ganin gaskiya?
Ka buge su, amma ba su ji zafi ba;
ka ragargaza su, amma suka ƙi su gyara.
Fuskarsu ta ƙeƙashe fiye da dutse
suka ƙi su tuba.
4 Na yi tunani, “Waɗannan ne kawai matalauta;
su wawaye ne,
gama ba su san hanyar Ubangiji ba,
ko abubuwan da Allahnsu yake bukata ba.
5 Saboda haka zan tafi wurin shugabanni
in yi musu magana;
tabbatacce sun san hanyar Ubangiji,
da abubuwan da Allahnsu yake bukata.”
Amma da nufi guda su ma suka karye karkiyar
suka tsintsinke sarƙoƙin.
6 Saboda haka zaki daga kurmi zai fāɗa musu,
kyarkeci kuma daga hamada zai cinye su,
damisa za tă yi musu ƙawanya kusa da garuruwansu
yă yayyage duk wanda ya kuskura ya fita,
gama tawayensu da girma yake
jan bayansu kuma yana da yawa.
7 “Me zai sa in gafarta muku?
’Ya’yanku sun yashe ni
sun yi rantsuwa da allolin da ba alloli ba ne.
Na biya musu dukan bukatunsu,
duk da haka suka yi zina
suka tattaru a gidajen karuwai.
8 An ciyar da su sosai, kamar ƙosassun ingarmu,
masu jaraba,
kowanne yana haniniya, yana neman matar maƙwabcinsa.
9 Ba zan hukunta su saboda wannan ba?” In ji Ubangiji.
“Bai kamata in yi ramuwa
a kan irin al’ummar nan ba?
10 “Ku ratsa cikin gonakin inabinta ku cinye su,
amma kada ku hallaka su gaba ɗaya.
Ku kakkaɓe rassanta,
gama waɗannan mutane ba na Ubangiji ba ne.
11 Gidan Isra’ila da gidan Yahuda
sun zama marasa aminci gaba ɗaya gare ni”
in ji Ubangiji.
12 Sun yi ƙarya a kan Ubangiji;
sun ce, “Ba zai yi kome ba!
Ba wata masifar da za tă same mu;
ba za mu taɓa ganin takobi ko yunwa ba.
13 Annabawa holoƙo ne kawai
maganar kuwa ba ta cikinsu;
saboda haka bari abin da suke faɗi ya koma kansu.”
14 Saboda haka ga abin Ubangiji Allah Maɗaukaki yana cewa,
“Domin mutanen sun yi waɗannan maganganu,
zan mai da maganata a bakinku wuta
waɗannan mutane kuwa su zama itacen da za tă ci.
15 Ya gidan Isra’ila,” in ji Ubangiji,
“Ina kawo al’umma daga nesa a kanku
al’umma ce ta tun dā mai ƙarfin hali,
mutane ne da ba ku san harshensu ba,
waɗanda ba za ku fahimci abin da suke faɗa ba.
16 Kwarinsu kamar buɗaɗɗen kabari ne;
dukansu jarumawa ne.
17 Za su cinye amfanin gonakinku da abincinku,
za su cinye ’ya’yanku maza da mata;
za su cinye garkunan tumakinku da na awakinku,
za su cinye ’ya’yan inabinku da na ɓaurenku.
Da takobi za su hallaka
biranenku masu katanga.
18 “Amma ko a cikin waɗancan kwanaki,” in ji Ubangiji, “ba zan hallaka ku gaba ɗaya ba.
19 Sa’ad da kuma mutanen suka yi tambaya, ‘Me ya sa Ubangiji Allahnmu ya yi dukan wannan gare mu?’ Sai ka amsa musu, ‘Yadda kuka yashe ni kuka kuma bauta wa baƙin alloli a ƙasarku, haka yanzu za ku bauta wa baƙi a ƙasar da ba taku ba.’
20 “Ka sanar da wannan ga gidan Yaƙub
ka yi shelarsa a Yahuda.
21 Ku ji wannan, ku wawaye marasa azanci,
waɗanda suke da idanu amma ba sa gani,
waɗanda suke da kunnuwa amma ba sa ji.
22 Bai kamata ku ji tsorona ba?” In ji Ubangiji.
“Bai kamata ku yi rawar jiki a gabana ba?
Na sa yashi ya zama iyakar teku,
madawwamiyar iyakar da ba zai tsallake ba.
Raƙuman ruwa za su iya yin hauka, amma ba za su iya haye ta ba;
za su iya yin ruri, amma ba za su iya ƙetare ta ba.
23 Amma mutanen nan suna da tauraren zukata, kuma ’yan tawaye ne;
sun kauce suka kuma rabu da ni.
24 Ba sa faɗa wa kansu, ‘Bari mu ji tsoron Ubangiji Allahnmu,
wanda yake ba mu ruwan sama a kan kari na kaka da na bazara,
wanda kullum yake tabbatar mana da girbi.’
25 Laifofinku sun raba ku da waɗannan abubuwa;
zunubanku sun hana ku samun alheri.
26 “A cikin mutanena an sami mugaye
waɗanda suke kwanton ɓauna kamar masu sa tarko wa tsuntsaye
kamar waɗanda suke kafa tarko don su kama mutane.
27 Kamar keji cike da tsuntsaye,
gidajensu sun cika da ruɗu;
sun yi arziki suka kuma zama masu iko
28 suka kuma yi ƙiba, suka yi bul-bul.
Mugayen ayyukansu ba su da iyaka;
ba sa wa marayu shari’ar adalci,
ba sa kāre ’yancin matalauta.
29 Bai kamata in hukunta su saboda wannan ba?”
In ji Ubangiji.
“Bai kamata in yi ramuwa
a kan irin al’umma kamar wannan ba?
30 “Abin banmamaki da bantsoro
ya faru a ƙasar.
31 Annabawa suna annabcin ƙarya,
firistoci suna mulki da ikon kansu,
mutanena kuma suna son haka.
Amma me za ku yi a ƙarshe?