19
Rabon don kabilar Simeyon
1 Ƙuri’a ta biyu ta fāɗa a kan kabilar Simeyon, bisa ga iyalansu. Ƙasarsu ta gādo tana cikin yankin Yahuda.
2 Waɗannan su ne wuraren da suka gāda.
Beyersheba (ko Sheba), Molada,
3 Hazar Shuwal, Bilha, Ezem,
4 Eltolad, Betul, Horma,
5 Ziklag, Bet-Markabot, Hazar-Susa,
6 Bet-Lebayot da Sharuhen, garuruwa goma sha uku ke nan da ƙauyukansu.
7 Akwai kuma Ayin, Rimmon, Eter da Ashan, garuruwa huɗu ke nan da ƙauyukansu,
8 da kuma dukan ƙauyukan da suke kewaye da garuruwan nan har zuwa Rama na Negeb (wato, Ba’alat-Beyer).
Wannan shi ne gādon kabilar Simeyon bisa ga iyalansu.
9 Daga cikin gādon mutanen Yahuda ne aka fitar da gādon kabilar Simeyon, bisa ga iyalansu, domin rabon da kabilar Yahuda suka samu ya fi ƙarfin abin da suke bukata. Saboda haka kabilar gādon Simeyon yana cikin harabar Yahuda.
Rabon da kabilar Zebulun ta samu
10 Ƙuri’a ta uku ta fāɗa a kan Zebulun bisa ga iyalansu.
Iyakar ƙasarsu ta gādo ta kai har Sarid.
11 Ta nufi yamma zuwa Marala, ta taɓa Dabbeshet, ta wuce zuwa rafin da yake kusa da Yokneyam.
12 Daga Sarid, ta juya gabas zuwa harabar Kislot Tabor, ta kuma wuce zuwa Daberat har zuwa Yafiya.
13 Sa’an nan ta ci gaba, ta yi gabas zuwa Gat-Hefer da Et Kazin; ta ɓulla a Rimmon, ta juya zuwa Neya.
14 A can ne iyakar ta kewaya zuwa Hannaton, sa’an nan ta ƙarasa a Kwarin Ifta El.
15 Zebulun ta ƙunshi garuruwa goma sha biyu da ƙauyukansu. Garuruwan sun haɗa da Kattat, Nahalal, Shimron, Idala da Betlehem.
16 Garuruwan nan da ƙauyukansu su ne gādon da kabilar Zebulun ta samu, bisa ga iyalansu.
Rabon da kabilar Issakar ta samu
17 Ƙuri’a ta huɗu ta fāɗa a kan kabilar Issakar, bisa ga iyalansu.
18 Ƙasarsu gādonsu ta haɗa da,
Yezireyel, Kessulot, Shunem,
19 Hafarayim, Anaharat,
20 Rabbat, Kishiyon, Ebez,
21 Remet, En Gannim, En Hadda da Bet-Fazez.
22 Iyakar ta taɓa Tabor Shahazuma da Bet-Shemesh ta kuma ƙarasa a Urdun.
Duka-duka garuruwa goma sha shida ke nan da ƙauyukansu.
23 Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne rabon da kabilar Issakar ta samu, bisa ga iyalansu.
Rabon da kabilar Asher ta samu
24 Ƙuri’a ta biyar ta fāɗa a kan kabilar Asher, bisa ga iyalansu.
25 Ƙasarsu gādonsu ta haɗa da,
Helkat, Hali, Beten, Akshaf,
26 Allammelek, Amad da Mishal. A arewanci kuma iyakar ta taɓa Karmel da Shihor Libnat.
27 Sai ta yi gabas zuwa Bet-Dagon, ta taɓa Zebulun da kuma Kwarin Ifta El, ta wuce arewa zuwa Bet-Emek da Neyiyel, ta wuce Kabul a hagu,
28 ta kai Abdon, Rehob, Hammon da Kana, har zuwa Sidon Babba.
29 Daga nan iyakar ta juya baya zuwa Rama, ta bi ta birnin nan mai katanga na Taya, ta juya ta nufi Hosa, sa’an nan ta ɓulla ta Bahar Rum cikin yankin Akzib,
30 Umma, Afek da Rehob.
Garuruwa ashirin da biyu ke nan da ƙauyukansu.
31 Garuruwan nan da ƙauyukansu su ne gādon da kabilar Asher ta samu bisa ga iyalansu.
Rabon da kabilar Naftali ta samu
32 Ƙuri’a ta shida ta fāɗa a kan kabilar Naftali, bisa ga iyalansu.
33 Iyakarsu ta kama daga Helef, daga babban itacen Mamre nan da yake a Za’anannim, ta wuce Adami Nekeb da Yabneyel zuwa Lakkum, ta kuma ƙarasa a Urdun.
34 Iyakar kuma ta juya yamma ta cikin Aznot-Tabo ta ɓulla a Hukkok. Ta taɓa Zebulun a kudu, Asher a yamma, da kuma Urdun a gabas.
35 Biranen da suke da katanga su ne Ziddim, Zer, Hammat, Rakkat, Kinneret,
36 Adama, Rama, Hazor,
37 Kedesh, Edireyi, En Hazor,
38 Yiron, Migdal El, Horem, Bet-Anat da Bet-Shemesh.
Garuruwa goma sha tara ke nan da ƙauyukansu.
39 Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne rabon da kabilar Naftali ta samu, bisa ga iyalansu.
Rabon da kabilar Dan ta samu
40 Ƙuri’a ta bakwai ta fāɗa a kan kabilar Dan, bisa ga iyalansu.
41 Ƙasarsu ta gādo ta haɗa da,
Zora, Eshtawol, Ir Shemesh,
42 Shalim, Aiyalon, Itla,
43 Elon, Timna, Ekron,
44 Elteke, Gibbeton, Ba’alat,
45 Yehud, Bene-Berak, Gat-Rimmon,
46 Me Yarkon da Rakkon tare da sashen da yake fuskantar Yaffa.
47 (Amma ya zama wa mutanen kabilar Dan da wahala su mallaki ƙasar da aka ba su gādo, saboda haka sai suka nufi Leshem suka ci su da yaƙi, suka karkashe mutanen wurin, suka mallake ta, suka zauna a ciki. Suka kuma sa wa Leshem, sunan kakansu, wato, Dan.)
48 Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne gādon kabilar Dan, bisa ga iyalansu.
Rabon da Yoshuwa ya samu
49 Sa’ad da aka gama raba gādon ƙasar bisa ga ƙuri’a. Sai Isra’ilawa suka ba Yoshuwa ɗan Nun nasa rabo a cikinsu,
50 yadda Ubangiji ya umarta, suka ba shi garin da ya ce a ba shi, Timnat Serad a ƙasar tudu ta Efraim. Ya kuma gina garin ya zauna a can.
51 Waɗannan su ne rabe-raben gādon da Eleyazar firist, Yoshuwa ɗan Nun, da kuma shugabannin kabilan iyalan Isra’ila suka rarraba ta hanyar jefa ƙuri’a a Shilo a gaban Ubangiji a ƙofar Tentin Sujada. Da haka suka yi suka gama rarraba ƙasar.