18
Misalin gwauruwa mai naciya
Yesu ya ba wa almajiransa wani misali, don yă koya musu yadda ya kamata su dinga yin addu’a kullum, ban da fasawa. Ya ce, “A wani gari, an yi wani alƙali wanda ba ya tsoron Allah, bai kuma kula da mutane ba. A garin nan kuma, akwai wata gwauruwa, wadda ta dinga zuwa wurin alƙalin nan, da roƙo cewa, ‘Ka yi mini adalci tsakanina da maƙiyina.’
“An daɗe yana ƙi, amma a ƙarshe ya ce cikin tunaninsa, ‘Ko da yake ba na tsoron Allah, ba na kuma kula da mutane ba, amma don gwauruwan nan ta dame ni, zan tabbatar cewa ta sami adalci, domin kada tă gajiyar da ni, da yawan zuwanta.’ ”
Sai Ubangiji ya ce, “Ku ji fa abin da alƙalin nan, marar gaskiya, ya ce. Ashe, Allah ba zai biya wa zaɓaɓɓunsa da suke masa kuka, dare da rana adalci ba? Zai ci gaba da ƙin sauraronsu ne? Ina gaya muku, zai tabbatar sun sami adalci, ban da ɓatan lokaci. Amma sa’ad da Ɗan Mutum ya dawo, zai sami bangaskiya a duniya ke nan?”
Misalin Bafarisiye da mai karɓar haraji
Yesu ya kuma faɗi wannan misali ga waɗansu masu taƙama da adalcinsu, kuma suna rena sauran mutane ya ce, 10  “Waɗansu mutane biyu sun tafi haikali don yin addu’a. Ɗaya Bafarisiye ne, ɗayan kuma mai karɓar haraji. 11  Sai Bafarisiyen ya tashi tsaye, ya yi addu’a game da kansa yana cewa, ‘Allah, na gode maka, saboda ni ba kamar sauran mutane ba ne, wato, mafasa, masu aikata mugunta, masu zina, ko kuma kamar mai karɓar harajin nan. 12  Ina azumi sau biyu a mako, ina ba da zakka daga kowane abin da na samu.’
13  “Amma mai karɓar harajin ya tsaya daga nesa. Bai ma iya ɗaga kansa sama ba, sai ya buga ƙirjinsa, yana cewa, ‘Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi ne.’
14  “Ina gaya muku, wannan mutum ne, ba ɗayan ba, ya koma gida baratacce, babu laifi a gaban Allah. Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Wanda kuma ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.”
Yesu da ƙananan yara
(Mattiyu 19.13-15; Markus 10.13-16)
15 Mutane suna kawo jarirai wurin Yesu don yă taɓa su. Da almajiransa suka ga haka, sai suka kwaɓe su. 16 Amma Yesu ya kira yaran a wurinsa ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina. Kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne. 17  Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ba zai karɓi mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, ba zai taɓa shiga mulkin ba.”
Mai mulki mai arziki
(Mattiyu 19.16-30; Markus 10.17-31)
18 Wani mai mulki ya tambayi Yesu ya ce, “Malam managarci, me zan yi don in gāji rai madawwami?”
19 Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake kira na managarci? Ai, ba wani nagari, sai Allah kaɗai. 20  Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ”
21 Mutumin ya ce, “Ai, tun ina ƙarami, na kiyaye duka waɗannan.”
22 Da Yesu ya ji haka, sai ya ce masa, “Akwai abu ɗaya har yanzu da ya rage maka. Ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, sa’an nan za ka sami dukiya a sama. Bayan haka, ka zo ka bi ni.”
23 Da jin haka, sai ya ɓata rai, domin shi mai arziki ne sosai. 24 Yesu ya kalle shi ya ce, “Yana da wuya fa, masu arziki su shiga mulkin Allah! 25  Tabbatacce, zai fi sauƙi raƙumi ya shiga ta kafar allura, da mai arziki ya shiga mulkin Allah.”
26 Waɗanda suka ji wannan suka yi tambaya suka ce, “To, wa zai iya samun ceto?”
27 Yesu ya amsa ya ce, “Abin da ba ya yiwuwa ga mutane, mai yiwuwa ne ga Allah.”
28 Sai Bitrus ya ce, masa, “To, ga shi mun bar kome da muke da shi, don mu bi ka!”
29 Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, ba wanda ya bar gida, ko mata, ko ’yan’uwa maza, ko iyaye, ko yara, saboda mulkin Allah, 30  da zai kāsa samun riɓi mai yawa, a wannan zamani, ya kuma sami rai madawwami a zamani mai zuwa.”
Yesu ya sāke magana a kan mutuwarsa
(Mattiyu 20.17-19; Markus 10.32-34)
31 Sai ya kai Sha Biyun gefe ɗaya, ya ce musu, “Za mu Urushalima, kuma dukan abin da annabawa suka rubuta a kan Ɗan Mutum zai cika. 32  Za a ba da shi ga Al’ummai, za su yi masa ba’a, su zage shi, su tofa masa miyau, 33  za su yi masa bulala, su kuma kashe shi. A rana ta uku kuma zai tashi.”
34 Almajiran ba su gane da ko ɗaya daga cikin wannan ba. An ɓoye musu ma’anarsa, kuma ba su gane da abin da yake magana a kai ba.
Makaho mai bara ya sami ganin gari
(Mattiyu 20.17-19; Markus 10.32-34)
35 Da Yesu ya yi kusa da Yeriko, akwai wani makaho da yake zaune a gefen hanya, yana bara. 36 Da ya ji taron suna wucewa, sai ya yi tambaya ko mene ne ke faruwa. 37 Suka ce masa, “Ai, Yesu Banazare ne ke wucewa.”
38 Sai ya yi kira ya ce, “Yesu, Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!”
39 Mutane da suke gaba suka kwaɓe shi, suka ce masa ya yi shiru. Amma sai ya ƙara ɗaga murya, yana cewa, “Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!”
40 Sai Yesu ya tsaya, ya ba da umarni a kawo mutumin wurinsa. Da ya zo kusa, Yesu ya tambaye shi ya ce, 41  “Me kake so in yi maka?”
Sai ya amsa ya ce, “Ubangiji, ina so in sami ganin gari.”
42 Yesu ya ce masa, “Ka sami ganin garinka; bangaskiyarka ta warkar da kai.” 43 Nan da nan, ya sami ganin garinsa, kuma ya bi Yesu, yana yabon Allah. Da dukan mutane suka ga wannan, sai su ma suka yabi Allah.