Makoki
1
1 Yanzu birnin ya zama babu kowa a ciki,
birnin da a dā yake cike da mutane!
Yanzu birnin ya zama kamar gwauruwa,
wadda a dā babba ce ita a cikin ƙasashe!
Ita da take sarauniya a cikin larduna
yanzu ta zama baiwa.
2 Tana yin kuka mai zafi da dare,
hawaye na gangara a kan kumatunta.
A cikin masoyanta duka
babu wanda ya yi mata ta’aziyya.
Duk abokanta sun yashe ta;
sun zama abokan gābanta.
3 Bayan wahala da baƙin ciki,
Yahuda ta tafi bauta.
Ta zauna a cikin ƙasashe,
ba tă samu wurin hutawa ba.
Duk masu fafararta sun same ta
sa’ad da take cikin matuƙar ɓacin rai.
4 Hanyoyin zuwa Sihiyona suna makoki,
gama ba wanda ya zo bikin da ta shirya.
Ba kowa a hanyoyin shiganta.
Firistocinta suna gurnani,
’yan matana kuma suna wahala,
kuma tana cikin shan wahala ƙwarai.
5 Maƙiyanta sun zama shugabanninta;
Abokan gābanta suna da kwanciyar rai.
Ubangiji ya kawo mata ɓacin rai
domin yawan zunubanta.
’Ya’yanta sun tafi bauta,
a ƙarƙashin maƙiyanta.
6 Diyar Sihiyona ba ta
da sauran daraja.
’Ya’yan sarakunanta sun zama kamar bareyi
waɗanda suka rasa wurin kiwo;
cikin rashin ƙarfi suka guje
wa masu fafararsu.
7 A cikin kwanakin da take shan wahala take kuma yawo
Urushalima ta tuna da dukan dukiyar
da take da ita a kwanakin dā can.
Sa’ad da mutanenta suka faɗa cikin hannun abokan gābanta,
ba wanda ya taimake ta.
Maƙiyanta suka dube ta
suka yi mata dariya don hallakar da ta auko mata.
8 Urushalima ta yi zunubi ƙwarai
saboda haka ta zama marar tsarki.
Dukan masu martaba ta sun raina ta,
gama sun ga tsiraicinta;
ita ma da kanta tana nishi da ƙyar
ta kuma juya baya.
9 Ƙazantarta ta manne wa rigunanta;
ba tă kula da nan gaba ba,
fāɗuwarta kuwa babban abu ne;
babu wanda zai yi mata ta’aziyya.
“Duba, ya Ubangiji, ka ga wahalata,
gama maƙiyi ya yi nasara.”
10 Maƙiya ya kwashe
dukiyarta duka;
ta ga mutanen da ba su san Allah ba
sun shiga wuri mai tsarkinta
waɗanda ka hana su
shiga taron jama’arka.
11 Dukan mutanenta suna nishi
da ƙyar suna neman burodi;
sun sayar da dukiyarsu don su samu abinci
don kada su mutu da yunwa.
“Ubangiji, ka duba ka gani,
gama an yashe ni.”
12 “Ko wannan ba wani abu ba ne a wurinku, dukanku masu wucewa?
Ku duba ku gani.
Ko akwai wata wahala kamar
irin wadda nake sha,
wadda Ubangiji ya auko mini
a cikin zafin fushinsa?
13 “Daga sama ya aiko da wuta,
ya aiko ta cikin ƙasusuwana.
Ya shimfiɗa raga a ƙafafuna
ya juyo da ni.
Ya bar ni ni kaɗai,
sumamme dukan yini.
14 “Ya ɗaura zunubaina a wuyana;
aka naɗe su a hannuwansa.
Aka rataye su a wuyana
Ubangiji ya kwashe ƙarfina.
Ya bashe ni
ga waɗanda suka fi ni ƙarfi.
15 “Ubangiji ya ƙi
duk mayaƙan da suke tare da ni;
ya sa wata runduna ta tayar mini
ta kuma tattake samarina.
Ubangiji ya tattake budurwa Diyar Yahuda
kamar ’ya’yan inabi a wurin matsewa.
16 “Dalilin da ya sa nake kuka ke nan
idanuna kuma suna ta zubar da hawaye.
Babu wani a kusa da zai yi mini ta’aziyya,
ba wanda zai sabunta ruhuna.
’Ya’yana sun zama fakirai
domin maƙiyina ya yi nasara.”
17 Sihiyona ta miƙa hannunta,
amma ba wani da zai yi mata ta’aziyya.
Ubangiji ya umarta cewa
maƙwabtansa za su zama maƙiyansa;
Urushalima ta zama
abar ƙyama a cikinsu.
18 “Ubangiji mai adalci ne,
duk da haka na yi tawaye da umarninsa.
Ku saurara, jama’a duka;
ku dubi wahalar da nake sha.
Samarina da ’yan matana
duka sun tafi bauta.
19 “Na kira abokaina
amma sun yashe ni.
Firistocina da dattawana
sun hallaka a cikin birnin
yayinda suke neman abinci
don kada su mutu da yunwa.
20 “Duba, Ubangiji, ka ga ƙuncin da nake ciki!
Ina shan azaba a raina,
ba ni da kwanciyar rai a cikin zuciyata,
domin na yi tawaye sosai.
A waje takobi na kisa;
a ciki kuma akwai mutuwa.
21 “Mutane suna ji ina nishi da ƙyar,
amma ba wanda zai yi mini ta’aziyya.
Dukan maƙiyana sun ji wahalar da nake ciki;
suna farin ciki da abin da ka yi.
Ka kawo ranan nan da ka sanar
domin su ma su zama kamar ni.
22 “Bari ka ga muguntarsu duka;
ka yi musu
yadda ka yi mini
domin dukan zunubansu.
Nishina da yawa
kuma zuciyata ta gaji.”