Mika
1
1 Maganar Ubangiji ta zo wa Mika mutumin Moreshet a zamanin Yotam, da na Ahaz, da kuma na Hezekiya, sarakunan Yahuda, Mika ya ga wahayi a kan Samariya da kuma a kan Urushalima. Ga abin da ya ce.
2 Ku ji, ya ku mutane duka,
ki saurara, ya ke duniya da dukan mazauna cikinki,
bari Ubangiji Mai Iko Duka yă zama shaida a kanku,
daga haikalinsa mai tsarki.
Hukunci a kan Samariya da kuma Urushalima
3 Duba! Ubangiji yana zuwa daga wurin zamansa;
zai sauko yă taka maɗaukakan wuraren duniya.
4 Duwatsu za su narke a ƙarƙashin ƙafafunsa,
kamar kaki a gaban wuta,
kwaruruka kuma za su ɓace,
kamar ruwan da yake gangarowa daga tsauni.
5 Duk wannan zai faru saboda laifin Yaƙub,
da kuma zunuban gidan Isra’ila ne.
Mene ne laifin Yaƙub?
Shin, ba Samariya ba ce?
Ina ne maɗaukakan wuraren Yahuda?
Shin, ba Urushalima ba ce?
6 “Saboda haka zan mai da Samariya tarin juji,
wurin noman inabi.
Zan zubar da duwatsunta a cikin kwari
in kuma bar harsashin gininta a bayyane.
7 Za a ragargaje dukan allolinta;
za a ƙone dukan baye-bayenta na haikali da wuta;
zan lalatar da dukan gumakanta.
Tun da ta wurin karuwanci ne ta tattara su,
ga karuwanci kuma za su koma.”
Kuka da Makoki
8 Saboda wannan zan yi baƙin ciki, in yi kuka;
zan yi tafiya ba takalmi, zan tuɓe, in kuma yi tafiya tsirara.
Zan yi kuka kamar dila,
in yi baƙin ciki kamar mujiya.
9 Gama raunin Samariya ba mai warkewa ba ne;
ya bazu har Yahuda.
Ya ma kai bakin ƙofar mutanena,
har ma Urushalima da kanta.
10 Kada a faɗe shi a Gat;
kada ma a yi kuka.
A maimako haka, a yi birgima a cikin ƙura
a Bet-Leyafra.
11 Ku wuce tsirara da kuma kunya,
ku mazaunan Shafir.
Bet-Ezel tana makoki
domin babu wani daga Za’anan
da ya fito don yă taimaka.
12 Mazaunan Marot
sun ƙosa su ga alheri,
amma Ubangiji ya sauko da azaba,
har zuwa ƙofar Urushalima.
13 Ku da kuke zama a Lakish,
ku ɗaura wa dawakai kekunan yaƙi.
Gama ku kuka fara yin zunubi
a Sihiyona,
gama an sami laifofin Isra’ila
a cikinku.
14 Saboda haka za ku ba da kyautan bankwana
ga Moreshet Gat.
Garin Akzib zai zama abin yaudara
ga sarakunan Isra’ila.
15 Ku mazaunan Maresha
Ubangiji zai kawo wanda zai ci ku da yaƙi.
Sarakunan Isra’ila
za su gudu zuwa Adullam.
16 Ku aske kanku ƙwal don makoki,
ku yi wa kanku ƙwalƙwal kamar ungulu.
Gama za a ja ’ya’yan da kuke farin ciki
a kai su bauta.