3
An Tsawata wa Shugabanni da Annabawa
Sa’an nan na ce,
“Ku kasa kunne, ku shugabannin Yaƙub,
ku masu mulkin gidan Isra’ila.
Ya kamata ku san shari’a,
ku da kuke ƙin abu mai kyau kuke ƙaunar mugunta,
ku da kuke feɗe mutanena
kuke tuge nama daga ƙasusuwansu;
ku da kuke cin naman mutanena,
ku feɗe fatar jikinsu
kuke kakkarya ƙasusuwansu,
kuke yayyanka su gunduwa-gunduwa kamar naman da za a toya,
kamar naman da za a sa a dafa.”
 
Sa’an nan za su kira ga Ubangiji,
amma ba zai amsa musu ba.
A wannan lokaci zai ɓoye fuskarsa daga gare su
saboda irin muguntar da suka yi.
Ga abin da Ubangiji ya faɗa,
“Game da annabawa
masu ɓad da mutanena,
in wani ya ciyar da su,
sai su ce akwai ‘salama’
amma in bai ciyar da su ba,
a shirye suke su kai masa hari.
Saboda haka dare yana zuwa a bisanku, ba tare da wahayi ba,
kuma duhu, ba tare da duba ba.
Rana za tă fāɗi wa annabawa,
yini kuma zai zama musu duhu.
Masu gani za su ji kunya,
masu duba kuma za su ji taƙaici.
Dukansu za su rufe fuskokinsu
gama ba amsa daga Allah.”
Amma game da ni, ina cike da iko
ta wurin Ruhun Ubangiji
da kuma adalci da ƙarfi,
don a sanar da Yaƙub laifofinsa,
ga Isra’ila kuma zunubinsa.
 
Ku ji wannan, ku shugabannin gidan Yaƙub,
ku masu mulkin gidan Isra’ila,
ku da kuke ƙyamar gaskiya,
kuka karkatar duk abin da yake na gaskiya;
10 kuka gina Sihiyona ta wurin zub da jini,
Urushalima kuma ta wurin mugunta.
11 Hukunce-hukuncen shugabannin ƙasar na cin hanci ne,
firistocinta kuma suna koyarwa don a biya su,
annabawanta kuwa suna yin annabci don neman kuɗi.
Duk da haka suna jingina a kan Ubangiji suna cewa,
“Ba Ubangiji yana tare da mu ba?
Ba bala’in da zai zo mana.”
12 Don haka, saboda ku,
za a nome Sihiyona kamar gona,
Urushalima kuma ta zama tarin juji,
tudun haikali kuwa zai zama kurmin ƙayayyuwa.