25
Misalin budurwai goma
1 “A lokacin mulkin sama zai zama kamar budurwai goma waɗanda suka ɗauki fitilunsu suka fita don su taryi ango.
2 Biyar daga cikinsu wawaye ne, biyar kuma masu hikima.
3 Wawayen sun ɗauki fitilunsu, sai dai ba su riƙe mai ba.
4 Masu hikimar kuwa suka riƙo tulunan mai da fitilunsu.
5 Ango ya yi jinkirin zuwa, sai duk suka shiga gyangyaɗi har barci ya kwashe su.
6 “Can tsakar dare, sai aka ji kira, ana cewa, ‘Ga ango nan! Ku fito, ku tarye shi!’
7 “Sai dukan budurwan nan suka farka suka kuna fitilunsu.
8 Sai wawayen suka ce wa masu hikimar, ‘Ku ɗan sassam mana manku; fitilunmu suna mutuwa.’
9 “Su kuwa suka amsa, suka ce, ‘A’a, wataƙila ba zai ishe mu da ku ba. Gara ku je wurin masu sayarwa ku sayo.’
10 “Amma yayinda suke kan tafiya garin sayen mai, sai ango ya iso. Budurwai da suke a shirye, suka shiga wajen bikin auren tare da shi. Aka kuma kulle ƙofa.
11 “An jima can, sai ga sauran sun iso. Suka ce, ‘Ranka yă daɗe! Ranka yă daɗe! Ka buɗe mana ƙofa!’
12 “Amma ya amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, ban san ku ba.’
13 “Saboda haka sai ku zauna a faɗake, don ba ku san ranar ko sa’ar ba.
Misalin talenti
(Luka 19.11-27)
14 “Har wa yau, za a kwatanta shi da mutumin da zai yi tafiya, wanda ya kira bayinsa ya kuma danƙa musu mallakarsa.
15 Ga guda, ya ba shi talenti biyar na kuɗi, ga wani talenti biyu, ga wani kuma talenti ɗaya, kowa bisa ga azancinsa. Sa’an nan ya yi tafiyarsa.
16 Mutumin da ya karɓi talenti biyar, nan da nan ya tafi ya yi kasuwanci da su har ya sami ribar talenti biyar.
17 Haka ma, wannan mai talenti biyu, shi ma ya yi riba biyu.
18 Amma mutumin da ya karɓi talenti ɗaya ɗin, ya tafi, ya tona rami, ya ɓoye kuɗin maigidansa.
19 “Bayan an daɗe, sai maigidan bayin nan ya dawo, ya kuma daidaita lissafi da su.
20 Mutumin da ya karɓi talenti biyar, ya kawo ƙarin talenti biyar. Ya ce, ‘Maigida, ka danƙa mini talenti biyar. Ga shi, na yi ribar biyar.’
21 “Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’
22 “Mutumin da yake da talenti biyu, shi ma ya zo ya ce, ‘Maigida, ka danƙa mini talenti biyu; ga shi, na yi ribar biyu.’
23 “Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’
24 “Sa’an nan mutumin da ya karɓi talenti ɗaya ya zo. Ya ce, ‘Maigida, na san cewa kai mutum ne mai wuyan sha’ani, kana girbi inda ba ka shuka ba, kana kuma tara inda ba ka yafa iri ba.
25 Saboda haka na ji tsoro, na je na ɓoye talentinka a ƙasa. Ga abinka.’
26 “Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Kai mugun bawa, mai ƙyuya! Ashe, ka san cewa ina girbi inda ban yi shuka ba, ina kuma tarawa inda ban yafa iri ba?
27 To, in haka ne, ai, da ka sa kuɗina a banki, don sa’ad da na dawo da na karɓi abina da riba.
28 “ ‘Karɓi talentin daga hannunsa ku ba wanda yake da talenti goma.
29 Gama duk mai abu za a ƙara masa, zai kuma same shi a yawalce. Duk wanda ba shi da shi kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa.
30 Ku jefar da banzan bawan nan waje, cikin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.’
Tumaki da awaki
31 “Sa’ad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukakarsa, tare da dukan mala’iku, zai zauna a kursiyinsa cikin ɗaukakar sama.
32 Za a tara dukan al’ummai a gabansa, zai kuma raba mutane dabam-dabam yadda makiyayi yakan ware tumaki daga awaki.
33 Zai sa tumaki a damansa, awaki kuma a hagunsa.
34 “Sa’an nan Sarki zai ce wa waɗanda suke damansa, ‘Ku zo, ku da Ubana ya yi wa albarka; ku karɓi gādonku, mulkin da aka shirya muku tun halittar duniya.
35 Gama da nake jin yunwa, kun ciyar da ni, da nake jin ƙishirwa, kun ba ni abin sha, da nake baƙunci, kun karɓe ni,
36 da nake bukatar tufafi, kun yi mini sutura, da na yi rashin lafiya, kun lura da ni, da nake kurkuku, kun ziyarce ni.’
37 “Sa’an nan masu adalci za su amsa masa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka da yunwa muka ciyar da kai, ko da ƙishirwa muka ba ka abin sha?
38 Yaushe kuma muka gan ka baƙo muka karɓe ka, ko cikin bukatar tufafi muka yi maka sutura?
39 Yaushe kuma muka gan ka cikin rashin lafiya ko a kurkuku muka ziyarce ka?’
40 “Sarkin zai amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka yi wa ɗaya daga cikin waɗannan ’yan’uwana mafi ƙanƙanta, ni kuka yi wa.’
41 “Sa’an nan zai ce wa waɗanda suke a hagunsa, ‘Ku rabu da ni, la’anannu, zuwa cikin madawwamiyar wutar da aka shirya don Iblis da mala’ikunsa.
42 Gama da nake jin yunwa, ba ku ba ni abinci ba, da nake jin ƙishirwa, ba ku ba ni abin sha ba,
43 da na yi baƙunci, ba ku karɓe ni ba, da nake bukatar tufafi, ba ku yi mini sutura ba, da na yi rashin lafiya kuma ina a kurkuku, ba ku lura da ni ba.’
44 “Su ma za su amsa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka cikin yunwa ko ƙishirwa ko baƙo ko cikin bukatar tufafi ko cikin rashin lafiya ko cikin kurkuku, ba mu taimake ka ba?’
45 “Zai amsa, yă ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafi ƙanƙanta ba, ba ku yi mini ba ke nan.’
46 “Sa’an nan za su tafi cikin madawwamiyar hukunci, amma masu adalci kuwa za su shiga rai madawwami.”