12
Firistoci da Lawiyawa
1 Waɗannan su ne firistoci da Lawiyawa waɗanda suka komo tare da Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel da kuma Yeshuwa.
Serahiya, Irmiya, Ezra,
2 Amariya, Malluk, Hattush
3 Shekaniya, Rehum, Meremot,
4 Iddo, Ginneton, Abiya,
5 Miyamin, Mowadiya, Bilga,
6 Shemahiya, Yohiyarib, Yedahiya,
7 Sallu, Amok, Hilkiya da Yedahiya.
Waɗannan su ne shugabannin firistoci da ’yan’uwansu a kwanakin Yeshuwa.
8 Lawiyawan su ne Yeshuwa, Binnuyi, Kadmiyel, Sherebiya, Yahuda, da kuma Mattaniya, wanda tare da ’yan’uwansa yake lura da waƙoƙin godiya.
9 Bakbukiya da Unni, ’yan’uwansu sun tsaya ɗaura da su a hidimomi.
10 Yeshuwa ne mahaifin Yohiyakim,
Yohiyakim shi ne mahaifin Eliyashib,
Eliyashib shi ne mahaifin Yohiyada,
11 Yohiyada shi ne mahaifin Yonatan,
Yonatan kuma mahaifin Yadduwa.
12 A kwanakin Yohiyakim, waɗannan su ne shugabannin iyalan firistoci,
na iyalin Serahiya, Merahiya;
na iyalin Irmiya, Hananiya;
13 na iyalin Ezra, Meshullam;
na iyalin Amariya, Yehohanan;
14 na iyalin Malluk, Yonatan;
na iyalin Shebaniya, Yusuf;
15 na iyalin Harim, Adna;
na iyalin Merahiyot, Helkai;
16 na iyalin Iddo, Zakariya;
na iyalin Ginneton, Meshullam;
17 na iyalin Abiya, Zikri;
na iyalin Miniyamin da na Mowadiya, Filtai;
18 na iyalin Bilga, Shammuwa;
na iyalin Shemahiya, Yehonatan;
19 na iyalin Yohiyarib, Mattenai;
na iyalin Yedahiya, Uzzi;
20 na iyalin Sallu, Kallai;
na iyalin Amok, Eber;
21 na iyalin Hilkiya, Hashabiya;
na iyalin Yedahiya, Netanel.
22 Shugabannin iyalin Lawiyawa a kwanakin Eliyashib, Yohiyada, Yohanan da Yadduwa, da kuma na firistoci, an rubuta su a zamanin mulkin Dariyus mutumin Farisa.
23 Shugabannin iyali cikin zuriyar Lawi har zuwa lokacin Yohanan ɗan Eliyashib, an rubuta su a cikin littafin tarihi.
24 Shugabannin Lawiyawa kuwa su ne Hashabiya, Sherebiya, Yeshuwa ɗan Kadmiyel, da ’yan’uwansu, waɗanda suka tsaya ɗaura da su don su yi yabo da kuma godiya, sashe ɗaya kan ba da amsa ga ɗaya sashen, kamar yadda Dawuda mutumin Allah ya umarta.
25 Mattaniya, Bakbukiya, Obadiya, Meshullam, Talmon da Akkub su ne matsaran ƙofofi waɗanda suka yi tsaron ɗaukan ajiya a ƙofofi.
26 Sun yi hidima a kwanakin Yohiyakim ɗan Yeshuwa, ɗan Yozadak, kuma a kwanakin Nehemiya gwamna da kuma na Ezra firist da kuma marubuci.
Keɓewar katangar Urushalima
27 A keɓewar katangar Urushalima, an nemi Lawiyawa daga inda suke zama aka kawo su Urushalima don su yi bikin miƙawa da farin ciki da waƙoƙin godiya da kuma kiɗin kuge, garaya da molo.
28 Aka kuma tattara mawaƙa su ma daga yankin kewayen Urushalima, daga ƙauyukan Netofawa,
29 daga Bet-Gilgal, da kuma daga wuraren Geba da Azmawet, gama mawaƙan sun gina wa kansu ƙauyuka kewaye da Urushalima.
30 Sa’ad da firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu da tsarki, sai suka tsarkake mutane, ƙofofi da kuma katanga.
31 Sai na sa shugabannin Yahuda suka haura zuwa bisan katangar. Na kuma sa manyan ƙungiyoyi biyu na mawaƙa su miƙa godiya. Ɗaya ya haura zuwa bisan katangar zuwa dama, wajen Ƙofar Juji.
32 Hoshahiya da rabin shugabannin Yahuda kuwa suka bi su,
33 tare da Azariya, Ezra, Meshullam,
34 Yahuda, Benyamin, Shemahiya, Irmiya,
35 da waɗansu firistoci kuma da ƙahoni, da kuma Zakariya ɗan Yonatan, ɗan Shemahiya, ɗan Mattaniya, ɗan Mikahiya, ɗan Zakkur, ɗan Asaf,
36 da ’yan’uwansa, Shemahiya, Azarel, Milalai, Gilalai, Ma’ai, Netanel, Yahuda da Hanani, tare da kayan kiɗi da Dawuda mutumin Allah ya umarta. Ezra malamin Doka ya jagoranci jerin gwanon.
37 A Ƙofar Maɓuɓɓuga suka ci gaba kai tsaye suka haura matakalan Birnin Dawuda a kan hawa zuwa katangar suka wuce a bisa gidan Dawuda zuwa Ƙofar Ruwa wajen gabas.
38 Ƙungiyar mawaƙa ta biyu suka yi jerin gwano a ɗaya gefen. Na bi su a bisan katangar, tare da rabin mutanen, muka wuce Hasumiya Tanderu zuwa Katanga Mai Faɗi,
39 bisa Ƙofar Efraim, Ƙofar Yeshana, Ƙofar Kifi, Hasumiyar Hananel da kuma Hasumiya ɗari, har zuwa Ƙofar Tumaki. A Ƙofar Matsara suka tsaya.
40 Ƙungiyoyin mawaƙa biyu da suka yi godiya suka ɗauki wurarensu a gidan Allah, haka ma ni, tare da rabin shugabanni,
41 da kuma firistoci, Eliyakim, Ma’asehiya, Miniyamin, Mikahiya, Eliyohenai, Zakariya da Hananiya tare da ƙahoninsu,
42 haka ma Ma’asehiya, Shemahiya, Eleyazar, Uzzi, Yehohanan, Malkiya, Elam da Ezer. Mawaƙan suka rera waƙoƙi a ƙarƙashin kulawar Yezrahiya.
43 A rana ta uku kuma suka miƙa manyan hadayu, suna farin ciki domin Allah ya ba su farin ciki mai girma. Mata da yara suka yi farin ciki su ma. An ji ƙarar farin ciki da ake yi a Urushalima daga nesa.
44 A lokacin an naɗa mutane su lura da ɗakunan ajiya don sadakoki, nunan fari da kuma zakka. Daga gonakin garuruwan da suke kewaye za su kawo sassan da Dokar ta umarta zuwa ɗakunan ajiya domin firistoci da Lawiyawa, gama Yahuda ya ji daɗin aikin firistoci da Lawiyawa.
45 Sun yi hidimar Allahnsu da kuma hidimar tsarkakewa, kamar yadda mawaƙa da matsaran ƙofofi suka yi, bisa ga umarnin Dawuda da ɗansa Solomon.
46 Gama tun dā, a kwanakin Dawuda da Asaf, akwai masu bi da mawaƙa da kuma na waƙoƙin yabo da na godiya ga Allah.
47 Saboda haka a kwanakin Zerubbabel da Nehemiya, dukan Isra’ila suka ba da sashe na kowace rana domin mawaƙa da matsaran ƙofofi. Suka kuma keɓe sashe don sauran Lawiyawa, Lawiyawan kuma suka keɓe sashe don zuriyar Haruna.