7
Bayan an sāke gina katangar na kuma sa ƙofofi a wurarensu, sai aka naɗa masu tsaro, da mawaƙa, da Lawiyawa. Na sa ɗan’uwana Hanani tare da Hananiya shugaban fada aikin riƙon Urushalima, domin shi Hananiya mutum mai mutunci ne, mai tsoron Allah fiye da yawancin mutane. Na ce musu, “Kada a buɗe ƙofofin Urushalima da sassafe sai rana ta fito sosai. Yayinda matsaran ƙofofi suna aiki, a kulle ƙofofin a sa musu sakata kafin matsaran su tashi, wajen fāɗuwar rana. Ku kuma naɗa mazaunan Urushalima a matsayin masu tsaro, waɗansunsu a wuraren aiki, waɗansun kuma kusa da gidajensu.”
Jerin sunayen waɗanda aka kai bauta da suka dawo
(Ezra 2.1-70)
Birnin Urushalima kuwa tana da fāɗi da girma, amma mutanen da suke zama a cikinta kaɗan ne, ba a kuma gina gidaje da yawa ba tukuna. Sai Allahna ya sa a zuciyata in tara manyan gari, shugabanni da talakawa don a rubuta su bisa ga iyalansu. Na sami littafin asali na waɗanda suka fara dawowa. Ga abin da na tarar an rubuta a ciki.
 
Waɗannan su ne mutanen yankin da suka dawo daga zaman bautar da Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kame (sun dawo Urushalima da Yahuda, kowanne zuwa garinsa. Sun dawo tare da Zerubbabel, da Yeshuwa, da Nehemiya, da Azariya, da Ra’amiya, da Nahamani, da Mordekai, da Bilshan, da Misfar, da Bigwai, da Nehum da kuma Ba’ana).
 
Ga jerin mutanen Isra’ila.
Zuriyar
Farosh mutum 2,172
ta Shefatiya 372
10 ta Ara 652
11 ta Fahat-Mowab (ta wurin Yeshuwa da Yowab) 2,818
12 ta Elam 1,254
13 ta Zattu 845
14 ta Zakkai 760
15 ta Binnuyi 648
16 ta Bebai 628
17 ta Azgad 2,322
18 ta Adonikam 667
19 ta Bigwai 2,067
20 ta Adin 655
21 ta Ater (ta wurin Hezekiya) 98
22 ta Hashum 328
23 ta Bezai 324
24 ta Harif 112
25 ta Gibeyon 95.
26 Mutanen
Betlehem da na Netofa 188
27 na Anatot 128
28 na Bet-Azmawet 42
29 na Kiriyat Yeyarim, Kefira da na Beyerot 743
30 na Rama da na Geba 621
31 na Mikmash 122
32 na Betel da na Ai 123
33 na ɗayan Nebo 52
34 na ɗayan Elam 1,254
35 na Harim 2 320
36 na Yeriko 345
37 na Lod, da na Hadid, da na Ono 721
38 na Sena’a 3,930.
 
39 Ga zuriyar Firistoci.
Zuriyar
Yedahiya (ta wurin iyalin Yeshuwa) 973
40 ta Immer 1,052
41 ta Fashhur 1,247
42 ta Harim 1,017.
 
43 Ga zuriyar Lawiyawa.
Zuriyar
Yeshuwa da Kadmiyel (ta wurin Hodeba) 74.
 
44 Mawaƙa.
Zuriyar
Asaf mutum 148.
 
45 Ga zuriyar Matsaran Ƙofofi.
Zuriyar
Shallum, Ater, Talmon,
Akkub, Hatita da Shobai 138.
 
46 Ma’aikatan haikali.
Zuriyar
Ziha, Hasufa, Tabbawot,
47 da ta Keros, da ta Siya, da ta Fadon,
48 da ta Lebana, da ta Hagaba, da ta Shalmai,
49 da ta Hanan, da ta Giddel, da ta Gahar,
50 da ta Reyahiya, da ta Rezin, da ta Nekoda,
51 da ta Gazzam, da ta Uzza, da ta Faseya,
52 da ta Besai, da ta Meyunawa, da ta Nefussiyawa,
53 da ta Bakbuk, da ta Hakufa, da ta Harhur,
54 da ta Bazlit, da ta Mehida, da ta Harsha,
55 da ta Barkos, da ta Sisera, da ta Tema,
56 da ta Neziya, da kuma ta Hatifa.
57 Ga zuriyar bayin Solomon.
Zuriyar
Sotai, da ta Soferet, da ta Ferida,
58 da ta Ya’ala, da ta Darkon, da ta Giddel,
59 Shefatiya, Hattil,
Fokeret-Hazzebayim, da Amon.
60 Zuriyar ma’aikatan haikali da ta bayin Solomon su 392.
 
61 Waɗansu sun hauro daga garuruwan Tel-Mela, Tel-Harsha, Kerub, Addon da Immer, amma ba su iya nuna cewa iyalansu su zuriyar Isra’ila ce ba,
62 zuriyar
Delahiya, Tobiya, da Nekoda 642.
 
63 Na wajen firistoci kuwa su ne,
Zuriyar
Hobahiya, da ta Hakkoz, da ta Barzillai (wani mutumin da ya auri ’yar Barzillai mutumin Gileyad, aka kuma kira shi da wannan suna).
64 Waɗannan ne aka nemi sunayensu a cikin tarihin asalin iyalai, amma ba a same su a ciki ba, saboda haka aka hana su shiga cikin firistoci, sun zama kamar marasa tsarki. 65 Sai gwamna ya umarce su kada su ci wani abinci mafi tsarki, sai akwai firist da zai nemi nufin Ubangiji ta wurin Urim da Tummim.
 
66 Yawan jama’ar duka ya kai mutum 42,360, 67 ban da bayinsu maza da mata 7,337. Suna kuma da mawaƙa maza da mata 245. 68 Akwai dawakai 736, alfadarai 245 69 raƙuma 435, da kuma jakuna 6,720.
 
70 Waɗansu shugabannin iyalai suka ba da kyautai domin taimakon aiki. Gwamna ya ba da darik 1,000 na zinariya, kwanoni 50, da riguna 530 don firistoci. 71 Waɗansu shugabannin iyalai sun ba da darik 20,000 na zinariya da mina 2,200 na azurfa don aiki. 72 Jimillar da sauran mutane suka bayar ta kai darik 20,000 na zinariya, minas 2,000 na azurfa, da riguna sittin da bakwai don firistoci.
73 Firistoci, da Lawiyawa, da matsaran ƙofofi, da mawaƙa, da ma’aikatan haikali tare da waɗansu mutane da kuma sauran mutanen Isra’ila, suka zauna a garuruwansu.
Ezra ya karanta Doka
Da wata na bakwai ya zo, Isra’ilawa kuwa sun riga sun zauna a garuruwansu,