2
Ninebe za tă fāɗi
Mai hari yana matsowa a kanki, Ninebe.
Ki tsare mafaka,
ki yi gadin hanya
ki sha ɗamara
ki tattaro dukan ƙarfinki!
 
Ubangiji zai maido da darajar Yaƙub,
kamar ta Isra’ila,
ko da yake masu washewa sun washe su
suka kuma lalatar da inabinsu.
 
Garkuwoyin sojojinsa ja wur ne;
jarumawansa suna sanye da kaya masu ruwan jan garura.
Ƙarafan kekunan yaƙi suna walƙiya
a ranar da aka shirya su;
ana kaɗa māsu da bantsoro.*
Kekunan yaƙi sun zabura a tituna,
suna kai da kawowa a dandali.
Suna walƙiya kamar tocila
suna sheƙawa a guje kamar walƙiya.
 
Ninebe ta tattara rundunarta,
duk da haka sun yi ta tuntuɓe a kan hanyarsu.
Sun ruga zuwa katangan birnin,
sun sanya garkuwar kāriya a inda ya kamata.
An buɗe ƙofofin rafuffukan
sai wurin ya rurrushe.
An umarta cewa birnin
za tă tafi bauta, za a kuma yi gaba da su.
Bayi ’yan mata suna kuka kamar tattabaru
suna buga ƙirjinsu.
Ninebe tana kama da tafki,
wanda ruwanta yana yoyo.
Suna kuka suna cewa, “Ku tsaya! Ku tsaya,”
amma ba wanda ya waiga.
A washe azurfa;
a washe zinariya;
dukiyarsu ba ta da iyaka,
arzikinsu kuma ba ya ƙarewa.
10 Ta zama wofi, an washe ta, an tuɓe ta!
Zukata sun narke, gwiwoyi suna kaɗuwa,
jikuna suna rawa, fuskoki duk sun kwantsare!
 
11 Ina kogon zakokin nan yake yanzu,
inda suka ciyar da ’ya’yansu,
inda zaki da zakanya sukan shiga,
da ’ya’yansu, ba mai damunsu
12 Zaki ya kashe abin da ya ishe ’ya’yansa
ya kuma murɗe wuyan dabbobi
ya cika wurin zamansa da abin da ya kama
ya cika kogwanninsa da abin da ya kashe.
 
13 “Ina gāba da ke,”
in ji Ubangiji Maɗaukaki.
“Zan ƙone kekunan yaƙinki,
takobi kuma zai fafare ’ya’yan zakokinki.
Ba kuma zan bar miki namun jejin da za ki kashe a duniya ba.
Ba kuwa za a ƙara jin
muryar ’yan saƙonki ba.”
* 2:3 Da Ibraniyanci; Seftuwajin da Siriyak / mahayan dawakai suna kai da kawowa 2:7 Ma’anar kalmar da Ibraniyanci babu tabbas.