21
An hallaka Arad
1 Sa’ad da sarkin Arad, mutumin Kan’ana, wanda yake zaune a Negeb, da ya ji cewa Isra’ila yana zuwa ta hanyar Atarim, sai ya fito, yă yaƙi Isra’ilawa, yă kuma kama waɗansunsu.
2 Sai Isra’ila suka yi alkawari wa Ubangiji suka ce, “In ka ba da waɗannan mutane a hannunmu, za mu hallaka dukan garuruwansu ƙaf.”
3 Ubangiji kuwa ya saurari kukan Isra’ila, ya kuma ba da Kan’aniyawa a gare su. Suka hallaka su da biranensu ƙaf; saboda haka aka sa wa wurin suna Horma.
Macijin tagulla
4 Suka kama hanya daga Dutsen Hor ta hanya zuwa Jan Teku, don su kauce wa Edom. Amma mutane suka rasa haƙuri a hanya;
5 suka yi wa Allah da Musa gunaguni, suka ce, “Me ya sa kuka fitar da mu daga Masar, kuka kawo mu mu mutu a wannan hamada? Babu abinci! Babu ruwa! Mu dai mun gaji da wannan abinci marar amfani!”
6 Sai Ubangiji ya aiko da macizai masu dafin a cikinsu, suka sassari mutane, Isra’ilawa masu yawa kuwa suka mutu.
7 Mutanen suka zo wurin Musa, suka ce, “Mun yi zunubi, da muka yi wa Ubangiji da kai gunaguni. Ka yi addu’a don Ubangiji yă ɗauke mana macizan nan.” Saboda haka Musa ya yi addu’a domin mutane.
8 Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ƙera siffar maciji ka rataye shi a bisa doguwar sanda; kowa da maciji ya sare shi, idan ya dubi macijin nan da ka rataye, zai rayu.”
9 Saboda haka Musa ya ƙera macijin tagulla, ya kuma rataye shi bisa doguwar sanda. Sa’an nan duk wanda maciji ya sare shi, ya kuma dubi macijin tagullar, zai warke.
Tafiya zuwa Mowab
10 Isra’ilawa suka kama hanya, suka yi sansani a Obot.
11 Sai suka tashi daga Obot, suka yi sansani a Iye Abarim a hamadar da take fuskantar Mowab, wajen fitowar rana.
12 Daga nan kuma suka ci gaba, suka yi sansani a Kwarin Zered.
13 Suka tashi daga nan, suka sauka kusa da Arnon wanda yake a hamadar da ta miƙe zuwa iyakar Amoriyawa. Arnon shi ne iyakar Mowab, wanda yake tsakanin Mowab da Amoriyawa.
14 Shi ya sa Littafin Yaƙoƙin Ubangiji ya ce,
“Waheb ta cikin yankin Sufa, da kwaruruka
na tuddan Arnon,
15 da gangaren kwaruruka,
wanda ya nausa zuwa garin Ar,
ya kuma dangana da kan iyakar Mowab.”
16 Daga can, suka gangara zuwa Beyer, wato, rijiyar da Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka tattara mutane duka, zan kuwa ba su ruwa.”
17 Sai Isra’ilawa suka rera wannan waƙa,
“Ki ɓuɓɓugo da ruwa, Ke rijiya!
Rera waƙa game da ita,
18 game da rijiyar da ’ya’yan sarki suka haƙa,
rijiyar da manyan mutane masu sandunan sarauta suka nuna da sandunansu.”
Sa’an nan suka tashi daga hamadar, suka tafi Mattana,
19 daga Mattana, suka tafi Nahaliyel, daga Nahaliyel, suka tafi Bamot,
20 daga Bamot kuma suka tafi kwarin da yake cikin Mowab inda ƙwanƙolin Fisga yake fuskantar hamada.
An ci Sihon da Og
(Maimaitawar Shari’a 2.26-37)
21 Isra’ila suka aiki manzanni wurin Sihon sarkin Amoriyawa su ce,
22 “Ka bari mu ratsa ta ƙasarka. Ba za mu shiga wata gona ba, ba za mu kuma shiga gonar inabi, ko mu sha ruwa daga wata rijiya ba. Za mu bi ta babbar hanyar sarki, har mu fita ƙasarka.”
23 Amma Sihon bai bar Isra’ila su ratsa ta yankinsa ba. Sai ya tara dukan sojojinsa, suka fita zuwa cikin hamada, su yaƙi Isra’ila. Da ya kai Yahaz, sai ya yaƙi Isra’ila.
24 Isra’ila fa suka kashe shi da takobi, suka ƙwace ƙasarsa, tun daga kogin Arnon har zuwa kogin Yabbok, zuwa kan iyakar Ammonawa kawai, gama sun yi wa iyakansu katanga.
25 Isra’ila suka ci dukan biranen Amoriyawa, suka kuma zauna a cikinsu, haɗe da babban birnin Heshbon da dukan ƙauyukanta.
26 Sihon sarkin Amoriyawa ya yi mulkin Heshbon, bayan ya ci sarkin Mowab na dā da yaƙi, ya kuma ƙwace dukan ƙasarsa har zuwa arewancin kogin Arnon.
27 Shi ya sa Amoriyawa suka rubuta wannan waƙa game da Heshbon suka ce,
“Ku zo mu sāke gina Heshbon,
birnin Sihon.
28 “Mayaƙansa sun fito kamar
harshen wuta
suka ƙone birnin Ar na Mowab
suna hallaka ’yan ƙasar
tuddan Arnon.
29 Kaitonki, Mowab!
Gunkinki Kemosh
ya yashe mutanenki;
aka kuma kama su, aka kai su bauta
wajen Sihon sarkin Amoriyawa.
30 “Amma mun tumɓuke su,
mun hallaka garuruwan Heshbon har zuwa Dibon.
Mun ragargaza su har zuwa Nofa
wanda ya miƙe zuwa Medeba.”
31 Ta haka Isra’ila suka zauna a ƙasar Amoriyawa.
32 Sai Musa ya aika ’yan leƙen asiri zuwa Yazer. Daga baya, sai Isra’ilawa suka ci ƙauyukan da suke kewaye, suka kuma kori Amoriyawa da suke zaune a can.
(Maimaitawar Shari’a 3.1-11)
33 Sai suka juya suka haura kan hanya ta zuwa Bashan, inda Og yake sarauta, ya kuwa fito tare da dukan sojojinsa suka yi yaƙi da Isra’ila a Edireyi.
34 Ubangiji ya ce wa Musa, “Kada ka ji tsoronsa, gama na ba da shi a gare ka, da dukan sojojinsa da kuma ƙasarsa. Ka yi da shi yadda ka yi da Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon.”
35 Ta haka suka kashe shi, tare da ’ya’yansa maza da kuma dukan sojojinsa, ba wanda ya ragu. Suka kuma mamaye ƙasarsa.