32
Kabilan hayen Urdun
(Maimaitawar Shari’a 3.12-22)
Mutanen Ruben da mutanen Gad, da suke da garken shanu da kuma garke tumaki masu yawa, suka ga cewa ƙasashen Yazer da Gileyad wurare ne masu kyau don kiwon shanu da tumaki. Saboda haka suka zo wurin Musa da Eleyazar da kuma shugabannin jama’a, suka ce, “Atarot, Dibon, Yazer, Nimra, Heshbon, Eleyale, Sebam, Nebo da Beyon, ƙasar da Ubangiji ya ci da yaƙi a gaban mutane Isra’ila, suna da kyau don dabbobi, bayinku kuma suna da dabbobi.” Suka ce, “In mun sami tagomashi daga gare ka bari a ba da wannan ƙasa ga bayinka, tă zama mallakanmu. Kada ka sa mu haye Urdun.”
Musa ya ce wa mutanen Gad da mutanen Ruben, “Wato, sai ’yan’uwanku su yi ta yaƙi ku kuwa ku zauna nan? Don me za ku karya zuciya Isra’ilawa daga hayewa zuwa ƙasar da Ubangiji ya ba su? Haka iyayenku suka yi sa’ad da na aike su daga Kadesh Barneya don su dubo ƙasar. Gama bayan suka haura Kwarin Eshkol suka hangi ƙasar, sai suka karya zuciyar Isra’ilawa daga shigar ƙasar da Ubangiji ya ba su. 10 A ranar kuwa Ubangiji ya husata har ya yi wannan rantsuwa cewa, 11 ‘Tabbatacce ba wani daga cikin mutanen da suka fito daga Masar, tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba, da zai ga ƙasar da na rantse zan ba Ibrahim, da Ishaku, da Yaƙub, domin ba su bi ni sosai ba, 12 ba ko ɗaya sai dai Kaleb ɗan Yefunne Bakenizze da Yoshuwa ɗan Nun, don su ne kaɗai suka bi Ubangiji da zuciya ɗaya.’ 13  Ubangiji ya husata da Isra’ila har ya sa suka yi ta yawo a hamada shekara arba’in, sai da dukan tsaran da suka aikata wannan mugunta a gabansa, suka mutu.
14 “Ga shi ku kuma, tarin masu zunubi, kuna tsaya a matsayin kakanninku, kuna sa Ubangiji yă sāke husata da Isra’ila. 15 In kun juye daga binsa, zai sāke barin dukan wannan mutane a hamada, ku ne kuwa za ku zama sanadin hallakarsu.”
16 Sai suka zo wurin Musa, suka ce, “Muna so mu gina katangar dutse don dabbobinmu, da kuma birane don matanmu da ’ya’yanmu a nan. 17 Matanmu da ’ya’yanmu za su zauna a biranen da suke da katanga, don kāriya daga mazaunan ƙasar, amma mu, za mu ɗauki makamai mu tafi tare da sauran Isra’ilawa, har mu kai su wuraren zamansu. 18 Ba za mu koma gidajenmu ba sai kowane mutumin Isra’ila ya sami gādonsa. 19 Ba za mu ci gādo tare da su a wancan hayin Urdun ba, domin mun sami gādonmu a wannan hayin gabashin Urdun.”
20 Sai Musa ya ce musu, “In za ku yi haka, in za ku sha ɗamara da makamai a gaban Ubangiji, ku tafi yaƙi, 21 in kuma dukanku za ku yi ɗamara, ku ɗauki makaman yaƙi a hayin Urdun a gaban Ubangiji har lokacin da ya kori abokan gābansa daga gabansa, 22 to, sa’ad da aka ci ƙasar a gaban Ubangiji, kwa kuɓuta daga alhakinku ga Ubangiji da kuma Isra’ila. Ƙasan nan kuwa za tă zama mallakarku a gaban Ubangiji.
23 “Amma in ba ku yi haka ba, kun yi zunubi ke nan ga Ubangiji; kuma ku san cewa zunubinku zai tone ku. 24 Ku gina birane domin matanku da ’ya’yanku, ku gina katanga kuma domin dabbobinku, amma fa ku cika abin da kuka yi alkawari.”
25 Mutanen Gad da mutanen Ruben, suka ce wa Musa, “Mu bayinka za mu yi yadda ranka yă daɗe ya umarta. 26 ’Ya’yanmu da matanmu, garkunan shanunmu da na tumakinmu, za su kasance a nan biranen Gileyad. 27 Amma bayinka, kowane mutum a cikinmu zai haye a gaban Ubangiji, zuwa yaƙi kamar yadda ranka yă daɗe ya faɗa.”
28 Sai Musa ya yi wa Eleyazar firist, da Yoshuwa ɗan Nun, da shugabannin gidajen kakannin kabilan mutanen Isra’ila kashedi a kansu, 29 ya ce, “In kowane sojan mutanen Gad da na mutanen Ruben, ya ɗauki makaman yaƙi, ya haye Urdun tare da ku a gaban Ubangiji, to, sa’ad da a ci ƙasar a gabanku, ku ba da ƙasar Gileyad tă zama mallakarsu. 30 Amma in ba su haye tare da ku da shirin yaƙi ba, to, sai ku ba su gādo a wancan haye kamar sauran kabilun a Kan’ana.”
31 Mutanen Gad da mutanen Ruben suka amsa, suka ce, “Barorinka za su yi abin da Ubangiji ya faɗa. 32 Za mu haye a gaban Ubangiji zuwa Kan’ana, amma mallakarmu ta gādo, za tă kasance a wannan hayi na Urdun.”
33 Sai Musa ya ba wa mutanen Gad, mutanen Ruben, da rabin mutanen Manasse ɗan Yusuf, masarautar Sihon, sarkin Amoriyawa, da masarautar Og na Bashan, dukan ƙasar, tare da biranenta da kuma yankunan da suke kewaye.
34 Mutanen Gad suka gina Dibon, Atarot, Arower, 35 Atrot Shofan, Yazer, Yogbeha, 36 Bet-Nimra, da Bet-Haran a matsayin birane masu katanga, suka kuma gina katanga don dabbobinsu. 37 Mutanen Ruben suka sāke gina Heshbon, Eleyale, da Kiriyatayim, 38 haka kuma suka gina Nebo da Ba’al-Meyon (an canja waɗannan sunaye) suka kuma gina Sibma. Suka ba wa biranen da suka sāke ginawa sunaye. 39 Zuriyar Makir ɗan Manasse suka tafi Gileyad, suka ci ta da yaƙi, suka kori mutanen Amoriyawa da suke can.
40 Saboda haka Musa ya ba da Gileyad ga mutanen Makir, zuriyar Manasse, suka kuma zauna a can. 41 Yayir, wani ɗan Manasse, ya ci ƙauyukansu da yaƙi, ya kuma ba su sunan Hawwot Yayir. 42 Noba kuma ya ci Kenat da ƙauyukanta da yaƙi, ya kuma ba ta suna Noba, bisa ga sunansa.