Karin Magana
Gabatarwa, manufa da kuma kan magana
1
1 Karin maganar Solomon ɗan Dawuda, sarkin Isra’ila.
2 Ga karin magana da za su taimake ka don samun hikima da horo;
don ganewa kalmomi masu zurfi;
3 don neman rayuwa ta horo da kuma ta hankali,
kana yin abin da yake daidai, mai adalci da kuma wanda ya dace;
4 don sa marar azanci yă yi hankali,
yă sa matasa su sani, su kuma iya rarrabewa,
5 bari masu hikima su saurara, su kuma ƙara ga saninsu,
bari masu tunani kuma su sami jagora,
6 don su fahimci karin magana da kuma misalai,
kalmomi da kuma kacici-kacici masu hikima.
7 Tsoron Ubangiji shi ne masomin ilimi,
amma wawaye sun rena hikima da horo.
Gargaɗi don a rungumi hikima
Jan kunne game da jaraba
8 Ɗana, ka saurari umarnin mahaifinka
kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.
9 Za su zama kayan ado don su inganta ka
da kuma sarƙar wuya don su yi wa wuyanka ado.
10 Ɗana, in masu zunubi sun jarabce ka,
kada ka yarda.
11 In suka ce, “Zo mu tafi;
mu yi kwanton ɓauna, mu nemi wani mu kashe,
mu fāɗa wa marasa laifi;
12 mu haɗiye su da rai gaba ɗaya kamar kabari,
kamar waɗanda suke gangarawa zuwa rami;
13 za mu sami dukiya masu daraja iri-iri,
mu kuma cika gidajenmu da ganima;
14 ka haɗa kai da mu,
za mu kuwa raba abin da muka sato”
15 ɗana, kada ka tafi tare da su,
kada ka taka ƙafarka a hanyarsu;
16 gama ƙafafunsu kan yi sauri ga yin zunubi,
suna saurin yin kisankai.
17 Ba shi da amfani a kafa tarko
a idanun dukan tsuntsaye!
18 Waɗannan irin mutane kansu suke kafa wa tarko;
ba sa kama kome, sai rayukansu!
19 Dukan waɗanda suke neman ribar da ba a samu a hanya mai kyau;
ƙarshen wannan yakan ɗauke rayukansu.
Jan kunne game da ƙin hikima
20 Hikima tana kira da ƙarfi a kan titi,
tana ɗaga muryarta a dandalin taron jama’a;
21 tana kira da ƙarfi a kan tituna masu surutu,
tana yin jawabinta a hanyoyin shiga gari.
22 “Har yaushe ku da kuke marasa azanci za ku ci gaba a hanyoyinku marasa azanci?
Har yaushe ku masu ba’a za ku yi ta murna cikin ba’arku
wawaye kuma ku ƙi ilimi?
23 Da a ce kun saurari tsawatata,
da na faɗa muku dukan abin da yake zuciyata
in kuma sanar da ku tunanina.
24 Amma da yake kun ƙi ni sa’ad da na yi kira
ba kuma wanda ya saurara sa’ad da na miƙa hannuna,
25 da yake kun ƙi dukan shawarata
ba ku kuma yarda da tsawatata ba,
26 Zan yi muku dariya sa’ad da masifa ta same ku,
zan yi muku ba’a sa’ad da bala’i ya same ku,
27 sa’ad da bala’i ya sha kanku kamar hadiri,
sa’ad da masifa ta share ku kamar guguwa,
sa’ad damuwa da wahala suka mamaye ku.
28 “Sa’an nan za su kira gare ni amma ba zan amsa ba;
za su neme ni amma ba za su same ni ba.
29 Da yake sun ƙi sani
ba su kuwa zaɓi tsoron Ubangiji ba,
30 da yake ba su karɓi shawarata ba
suka kuwa yi kunnen ƙashi ga tsawatata,
31 za su sami sakayyar abubuwan da suka yi
su kuma ƙoshi da sakayyar makircinsu.
32 Gama rashin hankalin marasa azanci zai kashe su,
rashin kulawar wawaye kuma zai hallaka su;
33 amma duk wanda ya saurare ni, zai zauna lafiya
yă kuma kasance da rai kwance, ba tare da tsoron lahani ba.”