19
Gara matalauci wanda yake marar laifi
da wawa wanda leɓunansa masu ƙarya ne.
 
Ba shi da kyau ka kasance da niyya babu sani,
ko ka kasance mai garaje ka ɓace hanya.
 
Wautar mutum kan lalatar da ransa,
duk da haka zuciyarsa kan ba wa Ubangiji laifi.
 
Wadata kan kawo abokai da yawa,
amma abokin matalauci kan bar shi.
 
Mai ba da shaidar ƙarya ba zai tafi babu hukunci ba,
kuma duk wanda ya baza ƙarairayi ba zai kuɓuta ba.
 
Kowa na ƙoƙari ya sami farin jini wurin mai mulki,
kuma kowa na so a ce shi abokin mutumin nan mai yawan kyauta ne.
 
’Yan’uwan matalauci sukan guje shi,
balle abokansa, su ma za su guje shi.
Ko da yake matalaucin yana binsu yana roƙo,
ba zai sam su ba.
 
Duk wanda ya sami hikima yana ƙaunar ransa;
duka wanda yake jin daɗi fahimi kan ci gaba.
 
Mai shaidar ƙarya ba zai tafi babu hukunci ba,
kuma duk mai baza ƙarairayi zai hallaka.
 
10 Bai dace da wawa ya yi rayuwa cikin jin daɗi ba,
haka ya fi muni bawa ya yi mulki a kan sarki!
 
11 Hikimar mutum kan ba shi haƙuri;
ɗaukakarsa ce ya ƙyale laifi.
 
12 Fushin sarki yana kama da rurin zaki,
amma tagomashinsa yana kama da raba a kan ciyawa.
 
13 Wawan yaro lalacin mahaifinsa ne,
mace mai yawan faɗa tana kama da ɗiɗɗigar ruwa.
 
14 Ana gādon dawakai da wadata daga iyaye ne,
amma mace mai basira daga Ubangiji ne.
 
15 Ragwanci kan jawo zurfin barci,
mutum mai sanyin jiki kuma yana tare da yunwa.
 
16 Duk wanda ya bi umarnai kan tsare ransa,
amma duk wanda ya ƙi binsu zai mutu.
 
17 Duk wanda yake kirki ga matalauta yana ba wa Ubangiji bashi ne,
zai kuwa sami lada game da abin da ya yi.
 
18 Ka hori ɗanka, gama yin haka akwai sa zuciya;
kada ka goyi baya lalacewarsa.
 
19 Dole mai zafin rai yă biya tara;
in ka fisshe shi sau ɗaya, to, sai ka sāke yin haka.
 
20 Ka kasa kunne ga shawara ka kuma yarda da umarni,
a ƙarshe kuwa za ka yi hikima.
 
21 Da yawa ne shirye-shiryen zuciyar mutum,
amma manufar Ubangiji ce takan cika.
 
22 Abin da mutum yake sha’awa shi ne ƙauna marar ƙarewa;*
gara ka zama matalauci da ka zama maƙaryaci.
 
23 Tsoron Ubangiji yakan kai ga rai.
Sa’an nan mutum ya sami biyan bukata, ba abin da zai cuce shi.
 
24 Rago kan sa hannunsa a kwano
ba ya ma iya ɗaga shi ya kai bakinsa!
 
25 Ka bulale mai ba’a, marasa azanci kuwa za su yi la’akari;
ka tsawata wa mai basira, zai kuwa ƙara sani.
 
26 Duk wanda ya yi wa mahaifinsa fashi ya kuma kori mahaifiyarsa
ɗa ne da kan kawo kunya da wulaƙanci.
 
27 In ka daina jin umarni, ɗana,
za ka kuwa kauce daga kalmomin sani.
 
28 Mai shaidar da yake malalaci yana wa shari’a ba’a ne,
bakin mugaye kuma na haɗiye mugunta.
 
29 An shirya tara saboda masu ba’a ne,
dūka kuma saboda bayan wawaye.
 
* 19:22 Ko kuwa Haɗamar mutum ita ce rashin kunyarsa