27
Kada ka yi fariya a kan gobe
gama ba san abin da ranar za tă kawo ba.
 
Ka bar wani ya yabe ka, ba kai kanka ba;
wani dabam, ba leɓunanka ba.
 
Dutse yana da nauyi yashi kuma wahala ce,
amma tsokanar wawa ta fi su duka nauyi.
 
Fushi mugun abu ne mai hallakarwa,
amma wa zai iya tsaya a gaban kishi?
 
Gara tsawatawar da ake yi a fili
da ƙaunar da ake yi a ɓoye.
 
Za a iya amince da rauni daga aboki,
amma abokin gāba ko da ya sumbace ka kada ka sake da shi!
 
Duk wanda ya ƙoshi da zuma, ba ya marmarinsa kuma
amma wanda yake yunwa ko abin da yake da ɗaci ma zai ji shi da zaƙi.
 
Kamar tsuntsun da ya ɓace daga sheƙarsa
haka yake da mutumin da ya bar gidansa.
 
Man shafawa mai ƙanshi da kuma turare kan faranta zuciya,
gaisuwar amini kuma takan fito daga shawarar kirki.
 
10 Kada ka manta da abokinka da kuma abokin mahaifinka,
kuma kada ka tafi gidan ɗan’uwanka sa’ad da masifa ta same ka,
gara ka je wurin maƙwabci na kusa da ka je wurin ɗan’uwan da yake da nisa.
 
11 Ka zama mai hikima, ɗana, ka kuma faranta mini zuciya;
zan iya amsa kowace irin suƙar da wani zai yi mini.
 
12 Mai basira kan hango hatsari ya kuma kauce,
marar azanci zai yi ta kutsa kai ciki, daga baya ya yi da na sani.
 
13 A karɓe rigunan wanda ya ɗauki lamunin baƙo;
a riƙe shi jingina in ya yi shi don mace marar aminci.
 
14 In mutum ya albarkaci maƙwabcinsa da murya mai ƙarfi da sassafe,
za a ɗauka shi a matsayin la’ana.
 
15 Mace mai fitina kamar
ɗiɗɗigar ruwa take ba ƙaƙƙautawa;
16 hana ta yana kamar yin ƙoƙari tsai da iska ne
ko yin ƙoƙarin cafke mai a tafin hannunka.
 
17 Kamar yadda ƙarfe kan wasa ƙarfe
haka mutum kan koyi daga mutum.
 
18 Duk wanda ya lura da itacen ɓaure, zai ci ’ya’yansa,
kuma duk wanda ya lura da maigidansa za a girmama shi.
 
19 Kamar yadda ruwa kan nuna yadda fuska take,
haka zuciyar mutum kan nuna irin mutumin.
 
20 Mutuwa da Hallaka* ba sa ƙoshi,
haka idanun mutum ba sa ƙoshi da gani.
 
21 Ana gwajin azurfa da kuma zinariya da wuta,
amma akan gwada mutum ta wurin yabon da ya samu.
 
22 Ko da ka daka wawa a turmi,
kana daka shi kamar hatsi da taɓarya,
ba za ka fid da wauta daga gare shi ba.
 
23 Ka tabbata ka san lafiyar garken tumakinka,
ka mai da hankali ga garken shanunka;
24 domin dukiya ba ta dawwama har abada,
ba a kuma kasance da rawani daga tsara zuwa tsara.
25 Sa’ad da aka yanki ingirci sabon toho kuma ya bayyana
aka kuma tattara ciyawa daga tuddai,
26 gashin raguna za su tanada maka tufafi,
za ka iya sayi gonaki masu kyau da kuɗin awaki.
27 Za ka kasance da madarar awaki mai yawa
don ka ciyar da kanka da kuma iyalinka
ka kuma inganta bayinka mata.
 
* 27:20 Da Ibraniyanci Sheol da Abaddon