29
Mutumin da ya ci gaba da taurinkai bayan an kwaɓe shi
ba da daɗewa ba zai hallaka ba makawa.
 
Sa’ad da masu adalci suke cin nasara, mutane kan yi farin ciki
sa’ad da mugaye suke mulki, mutane kan yi nishi.
 
Duk mai ƙaunar hikima kan kawo wa mahaifinsa farin ciki,
amma wanda yake ma’amala da karuwai kan lalatar da dukiyarsa.
 
Ta wurin yin adalci sarki kan sa ƙasa tă yi ƙarƙo
amma duk mai haɗama don cin hanci kan rushe ƙasar.
 
Duk wanda yake wa maƙwabcinsa daɗin baki
yana sa wa ƙafafunsa tarko ne.
 
Mugun mutum tarko ne ta wurin zunubinsa,
amma mai adalci zai iya rera ya kuma yi murna.
 
Masu adalci sun damu game da adalci don talakawa,
amma mugaye ba su da wannan damuwa.
 
Masu ba’a kan kuta faɗa a birni,
amma masu hikima sukan kwantar da fushi.
 
In mai hikima ya je wurin shari’a da wawa,
wawa kan yi ta fushi yana ta dariya, ba kuwa za a sami salama ba.
 
10 Masu kisankai sukan ƙi mutum mai mutunci
su kuma nema su kashe mai aikata gaskiya.
 
11 Wawa yakan nuna fushinsa a fili,
amma mai hikima kan kanne fushinsa.
 
12 In mai mulki yana sauraran ƙarairayi,
dukan ma’aikatansa za su zama mugaye.
 
13 Matalauci da azzalumi suna da wannan abu ɗaya.
Ubangiji ne yake ba dukansu gani.
 
14 In sarki yana hukunta talakawa da adalci
kursiyinsa kullum zai kasance lafiya.
 
15 Sandar gyara kan ba da hikima,
amma yaron da aka bari ba horo kan jawo kunya ga mahaifiyarsa.
 
16 Sa’ad da mugaye suke cin nasara, haka zunubi zai yi ta ƙaruwa,
amma masu adalci za su ga fāɗuwar waɗannan mutane.
 
17 Ka hori ɗanka, zai kuwa ba ka salama;
zai ba ka farin cikin da kake so.
 
18 Inda ba wahayi, mutane kan kangare;
amma masu albarka ne waɗanda suke kiyaye doka.
 
19 Ba a yi wa bawa gyara ta wurin magana kawai;
ko da ya fahimta ma, ba zai kula ba.
 
20 Ka ga mutum mai yin magana da garaje?
To, gara a sa zuciya ga wawa da a sa zuciya gare shi.
 
21 In mutum ya yi wa bawansa shagwaɓa tun yana yaro,
zai jawo baƙin ciki a ƙarshe.
 
22 Mutum mai cika fushi yakan tā da faɗa,
mai zafin rai kuma kan yi zunubai masu yawa.
 
23 Fariyar mutum kan jawo masa ƙasƙanci
amma mai sauƙinkai kan sami girmamawa.
 
24 Duk wanda yake abokin ɓarawo abokin gāban kansa ne;
yana jin sa yana ta rantsuwa, amma bai isa ya ce kome ba.
 
25 Jin tsoron mutum tarko ne,
amma duk wanda ya dogara ga Ubangiji zai zauna lafiya.
 
26 Mutane sukan nemi samun farin jini daga wurin sarki,
amma daga wurin Ubangiji ne mutum kan sami adalci.
 
27 Masu adalci suna ƙyamar masu rashin gaskiya;
mugaye sukan yi ƙyamar masu aikata gaskiya.