Zabura 108
Waƙa ce. Zabura ta Dawuda.
Zuciyata tsayayyiya ce, ya Allah;
zan rera in kuma yi kiɗi da dukan raina.
Ku farka, garaya da molo!
Zan farkar da rana.
Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai;
zan rera game da kai cikin mutane.
Gama ƙaunarka da girma take, bisa fiye da sammai;
amincinka ya kai sarari.
A ɗaukaka ka, ya Allah, a bisa sammai,
bari kuma ɗaukakarka ta kasance a bisa dukan duniya.
 
Ka cece mu ka kuma taimake mu da hannunka na dama,
domin waɗanda kake ƙauna su kuɓuta.
Allah ya yi magana daga wurinsa mai tsarki,
“Ciki nasara zan raba Shekem
in kuma auna Kwarin Sukkot.
Gileyad nawa ne, Manasse nawa ne;
Efraim shi hulan kwanona,
Yahuda ne sandana na sarauta.
Mowab shi ne kwanon wankina,
a kan Edom zan jefa takalmina;
a bisa Filistiya zan yi kirari cikin nasara.”
 
10 Wa zai kawo ni birni mai katanga?
Wa zai jagorance ni zuwa Edom?
11 Ba kai ba ne, ya Allah, kai da ka ƙi mu
ba ka kuwa fita tare da mayaƙanmu?
12 Ka ba mu taimako a kan abokin gāba,
gama taimakon mutum banza ne.
13 Tare da Allah za mu yi nasara,
zai kuma tattaka abokan gābanmu.