Zabura 11
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don busa. Ta Dawuda.
A wurin Ubangiji ne nake samun mafaka.
Yaya za ku ce mini,
“Ka yi firiya kamar tsuntsu zuwa duwatsu.
Gama duba, mugaye sun tanƙware bakkunansu;
sun kuma ɗana kibiyoyinsu
don su harbi mutanen kirki a zuciya
daga cikin duhu.
Sa’ad da aka tumɓuke tushe,
me adali zai iya yi?”
 
Ubangiji yana cikin haikalinsa mai tsarki;
Ubangiji yana a kursiyinsa a sama.
Yana kallon ’ya’yan mutane;
idanunsa suna bincike su.
Ubangiji yana bincike adalai,
amma ransa yana ƙi mugaye
da masu son rikici.
A kan mugaye zai zuba
garwashin wuta mai zafi da kuma kibiritu;
iska mai zafi zai zama rabonsu.
 
Gama Ubangiji mai adalci ne,
yana ƙaunar gaskiya
masu adalci za su ga fuskarsa.