Zabura 120
Waƙar haurawa.
Na yi kira ga Ubangiji cikin damuwata,
ya kuwa amsa mini.
Ka cece ni, ya Ubangiji,
daga leɓuna masu ƙarya
da kuma daga harsuna masu yaudara.
 
Me zai yi maka,
me kuma ya fi,
ya kai harshe mai yaudara?
Zai hukunta ku da kibiyoyi masu tsini na jarumi,
tare da garwashin wuta na itacen tsintsiya.
 
Kaitona da nake zama a Meshek,
da nake zama a ciki tentunan Kedar!
Da daɗewa na zauna
a cikin waɗanda suke ƙin salama.
Ni mutum ne mai salama;
amma sa’ad da na yi magana, su sai su yi ta yaƙi.