Zabura 123
Waƙar haurawa.
Na tā da idanuna gare ka,
gare ka da kursiyinka yake cikin sama.
Kamar yadda idanun bayi suna duban hannun maigidansu,
kamar yadda idanun baiwa suna duban hannun uwargijiyarta,
haka idanunmu suna duban Ubangiji Allahnmu,
sai ya nuna mana jinƙansa.
 
Ka yi mana jinƙai, ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai,
gama mun jimre da reni mai yawa.
Mun jimre da wulaƙanci
daga masu girman kai,
reni mai yawa daga masu fariya.