Zabura 130
Waƙar haurawa.
Daga cikin zurfafa na yi kuka gare ka, ya Ubangiji;
Ya Ubangiji, ka ji muryata.
Bari kunnuwanka su saurara
ga kukata ta neman jinƙai.
 
In kai, ya Ubangiji, za ka lissafta zunubai,
Ya Ubangiji, wa zai tsaya?
Amma tare da kai akwai gafartawa,
saboda haka ake tsoronka.
 
Zan jira Ubangiji, raina zai jira,
kuma a cikin maganarsa na sa zuciyata.
Raina na jiran Ubangiji
fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya,
fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya.
 
Ya Isra’ila, sa zuciya ga Ubangiji,
gama tare da Ubangiji akwai ƙauna marar ƙarewa
kuma tare da shi akwai cikakkiyar fansa.
Shi kansa zai fanshi Isra’ila
daga dukan zunubansu.