Zabura 138
Ta Dawuda.
Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata;
a gaban “alloli” zan rera yabo.
Zan rusuna ta wajen haikalinka mai tsarki
zan kuma yabi sunanka
saboda ƙaunarka da amincinka,
saboda ka ɗaukaka a bisa kome
sunanka da kuma maganarka.
Sa’ad da na kira, ka amsa mini;
ka sa na zama mai ƙarfin hali ka kuma ƙarfafa ni.
 
Bari dukan sarakunan duniya su yabe ka, ya Ubangiji,
sa’ad da suka ji maganganun bakinka.
Bari su rera game da hanyoyin Ubangiji,
gama ɗaukakar Ubangiji da girma take.
 
Ko da yake Ubangiji yana bisa, yakan dubi kāsassu,
amma tun da nesa ya san masu girman kai.
Ko da na yi tafiya a tsakiyar wahala,
kana kiyaye raina;
ka miƙa hannunka a kan fushin maƙiyana,
da hannunka na dama ka cece ni.
Ubangiji zai cika manufarsa a kaina;
ƙaunarka, ya Ubangiji, madawwamiya ce har abada,
kada ka ƙyale ayyukan hannuwanka.