Zabura 16
Miktam ne* na Dawuda.
Ka kiyaye ni, ya Allah,
gama a cikinka nake samun mafaka.
 
Na ce wa Ubangiji, “Kai ne shugabana;
in ba tare da kai ba, ba ni da wani abu mai kyau.”
Game da tsarkakan da suke cikin ƙasar kuwa,
su ne masu ɗaukakar da dukan farin cikina ya dangana.
Baƙin ciki zai ƙaru wa waɗanda suke bin waɗansu alloli.
Ba zan zuba musu hadayarsu ta jini ba
ko in ambaci sunayensu da bakina.
 
Ubangiji, ka ba ni rabona da kwaf ɗin na;
ka kiyaye rabona,
Iyakoki sun fāɗo mini a wurare masu daɗi;
tabbatacce ina da gādo mai bansha’awa.
Zan yabi Ubangiji, wanda yake ba ni shawara;
ko da dare ma zuciyata kan koya mini.
Kullum nakan sa Ubangiji a gabana.
Gama yana a hannun damana, ba zan jijjigu ba.
 
Saboda haka zuciyata tana murna harshena kuma yana farin ciki;
jikina kuma zai zauna lafiya,
10 domin ba za ka yashe ni a kabari ba,
ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka yă ruɓa ba.
11 Ka sanar da ni hanyar rai;
za ka cika ni da farin ciki a gabanka,
da madawwamin jin daɗi a hannun damarka.
* Zabura 16: Kan magana, mai yiwuwa wata kalma ta kiɗa ce.