Zabura 19
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.
Sammai suna shelar ɗaukakar Allah;
sararin sama suna furta aikin hannuwansa.
Kowace rana tana yin jawabi;
kowane dare yana nuna sani.
Ba magana, ba kalmar da aka hurta,
ba wani amon da aka ji daga gare su.
Duk da haka muryarsu tana kaiwa ga dukan duniya,
kalmominsu zuwa iyakokin duniya.
A sammai Allah ya kafa tenti domin rana,
wanda yake kamar ango mai fitowa daga rumfarsa,
kamar gwani ɗan wasan da yake farin ciki yă yi tsere.
Takan taso daga ƙarshen sammai
ta kewaye zuwa wancan;
babu abin da yake ɓuya wa zafinta.
 
Dokar Ubangiji cikakkiya ce,
takan wartsakar da rai.
Farillan Ubangiji abin dogara ne,
suna mai da hikima da sauƙi.
Ƙa’idodin Ubangiji daidai ne,
suna ba da farin ciki ga zuciya.
Umarnan Ubangiji haske ne
suna ba da haske ga idanu.
Tsoron Ubangiji yakan kawo tsabtar zuciya,
zai kasance har abada.
Farillan Ubangiji tabbatattu ne,
kuma gaba ɗaya masu adalci ne.
 
10 Sun fi zinariya daraja,
fiye da zalla zinariya nesa;
sun fi zuma zaƙi
fiye da zuma daga kaki.
11 Ta wurinsu ana gargaɗe bawanka;
a kiyaye su akwai lada mai girma.
12 Wane ne zai iya rabe kurakuransa?
Ya gafarta ɓoyayyun laifofinsa.
13 Ka kiyaye bawanka daga zunubin ganganci;
kada ka bari su yi mulki a kaina.
Ta haka zan zama marar laifi;
marar laifi na babban tawaye.
 
14 Bari kalmomin bakina da tunanin zuciyata
su zama abin gamsuwa a gabanka,
Ya Ubangiji, Dutsena da Mai fansata.